'Akwai sauran Ƴan Ta'adda,' Malami Ya Fadi Kuskuren Tinubu a Jawabin 1 ga Oktoba
- Bishop Mathew Kukah ya ce Najeriya ba za ta iya kawo ƙarshen ta'addanci da karfin soja kaɗai ba, domin bindiga ba ta kawar da akida
- Malamin cocin ya yi kira da a rungumi sulhu, shugabanci nagari, da adalci domin magance tushen rashin tsaro da tashe tashen hankula
- Ya gargadi Shugaba Bola Tinubu cewa ci gaban tsaro da ake gani a yanzu na wucin gadi ne, ba wai an kawo karshen matsalar kenan ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban cocin Katolika a Sokoto, Most Rev. Matthew Hassan Kukah, ya ce Najeriya ba za ta iya kawo ƙarshen ta’addanci da yaƙi kaɗai ba.
Babban malami ya ce dole sai Najeriya ta rungumi sulhu da wasu dabaru da ba na amfani da karfin bindiga ba wajen magance tushen matsalar tsaro.

Kara karanta wannan
"Akwai rikitarwa," Jonathan ya bayyana abin da mutane ba su sani ba game da Boko Haram

Source: Twitter
Sojoji kadai ba za su iya magance tsaro ba
Ya faɗi haka ne a Abuja yayin kaddamar da wani littafi da tsohon shugaban tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta, inji rahoton Zagazola Makama.
Bishop Kukah ya jaddada cewa dogaro da dabarun soja da maimaita hare-haren kawar da ta’addanci ba sa samar da zaman lafiya mai dorewa.
Ya ce Boko Haram ba ƙungiya ce mai ɗauke da makamai kawai ba, bugu da ƙari, masu aƙidar riƙau ce da ke ci gaba da ƙarfafa gwiwar magoya bayanta.
“Sanin kowa ne cewa tsawon shekaru dakarun Operation Lafiya Dole, Operation Restore Order, Operation Hadin Kai, Operation Safe Haven da sauransu ke yaki da 'yan ta'adda.
"Yayin da duk ɗaya ta gaza, sai a ƙaddamar da wata rundunar. Amma wannan bai kawo ƙarshen ta’addanci ba saboda ba za ka iya yakar akida da bindiga kaɗai ba."
- Most Rev. Matthew Hassan Kukah.
Muhimmancin sulhu da yiwa kowa adalci
Mathew Kukah ya ce kalubalen ba wai kawai yaƙar mayaƙan Boko Haram a filin daga ba ne, illa fahimtar “akidarsu ta rayuwa da mutuwa.”
Shugaban cocin Katolika a Sokoto, ya jaddada cewa amfani da karfin bindiga ba zai iya gina zaman lafiya ba, dole sai an yi amfani da dabarun sulhu da riko da adalci.
Bishop ɗin ya ambaci babi na 11, 12 da 13 na littafin Irabor, inda aka mayar da hankali kan sulhu, shugabanci na gari, adalci da warkar da ƙasa a matsayin muhimman sharudda don gyaran tsaro.
Ya yi nuni da cewa littafin Janar Irabor ya zarce littafi kan dabarun soja, a cewarsa, littafin ya fito da muhimmancin tattaunawa, gyare-gyare da sabuwar akidar yaki da ta'addanci.

Source: Twitter
“An samu tsaro na wucin gadi' - Kukah
A wata tattaunawa da Arise News, Bishop Kukah ya ce Najeriya ta shiga wani yanayi na raguwar rikice-rikice na ɗan lokaci, amma hakan ba yana nufin matsalar tsaro ta ƙare ba.

Kara karanta wannan
Taron tsintsiya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi kallon da Tinubu ke yi wa 'yan hadaka
Ya yi gargadin cewa jawabin Shugaba Bola Tinubu na cewar barazanar tsaro ta ƙare a Najeriya, na iya zama saduda ba tare da sanin gobe ba.
“Ina kira da a zuba jari a ci gaban ɗan Adam, sulhu, da gina amana a hukumomi. Bindigogi na iya samar da sauki, amma ra’ayoyi da adalci ne kawai za su tabbatar da zaman lafiya."
- Most Rev. Matthew Kukah.
'Yakin ba na soja kadai ba ne' - Buratai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon hafsan sojojin ƙasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ba gwamnati shawara kan murkushe 'yan ta'adda.
Tukur Buratai ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta yi amfani da tsarin da ta yi amfani da shi a lokacin COVID-19 wajen dawo da tsaro.
Tsohon babban hafsan sojin ya jaddada cewa haɗin kai, wayar da kai da tsare-tsaren dogon lokaci ne kaɗai za su taimaka wajen murkushe ‘yan ta’adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
