Daga zuwa Haduwa da Saurayi, Wata Yar Amurka Ta Mutu a Yanayi Mai Ban Mamaki a Najeriya
- Yan sanda sun fara bincike kan mutuwa mai ban mamaki da wata 'yar Amurka ta yi lokacin da ta zo Najeriya domin haduwa da saurayinta
- Matar yar shekara 60 a duniya, Jacqueline Bolling Elton ta mutu ne a asibiti bayan ta kamu da rashin lafiyar da har yanzu ba a gano ba
- Rundunar Yan Sanda ta ajiye gawar matar a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin Warri, ta kuma kama saurayin mamaciyar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Warri, jihar Delta - Wata mata 'yar asalin kasar Amurka, Jacqueline Bolling Elton ta mutu a Najeriya bayan ta kawo wa saurayinta ziyara.
Matar mai shekaru 60 da haihuwa ta rasa ranta ne a wani yanayi mai ban mamaki lokacin da ta zo Najeriya domin haduwa da saurayinta a Warri, jihar Delta.

Source: Original
Rundunar ’Yan sandan Jihar Delta ta ce tana binciken mutuwar 'yar Amurkan domin gano ainihin abin da ya faru, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yar Amurka ta mutu a wurin saurayinta
Rahotanni sun bayyana cewa Elton ta rasu ne a gidan saurayinta mai shekaru 39, Alawode Olaide a birnin Warri da ke kudancin Najeriya.
Marigayiyar ta isa Warri ne a ranar 15 ga Satumba, 2025, domin daukar wani lokaci tare da masoyinta Olaide, wanda ta fara haɗuwa da shi a shafin sada zumunta har suka fara soyayya.
Sai dai a ranar 29 ga Satumba 2025, kimanin ƙarfe 3:00 na rana, matar ta fara rashin lafiya ba tare da zato ba, inda aka gaggauta kai ta asibitin kudi a Otokutu, kusa da Warri.
Yadda matar ta mutu a asibiti a jihar Delta
Wata majiya ta ce:
“Daga baya aka tura ta zuwa Asibitin Gwamnati na Warri, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta tun kafin a shigar da ita dakin kwantar da marasa lafiya.
“An ajiye gawarta a dakin ajiyar gawa na Asibitin Warri domin yin gwaji. Kuma tuni aka sanar da jami’an ’yan sanda game da lamarin, inda suka kai ziyara wajen kuma suka kama Olaide domin bincike."
Wane mataki 'yan sanda suka dauka?
Wata majiya ta daban ta ƙara da cewa rundunar yan sanda za ta mika lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Jihar (SCID) domin zurfafa bincike.
Da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar ’yan sanda a Jihar Delta, SP Bright Edafe, ya tabbatar da mutuwar da kuma kama wanda ake zargi.
SP Edafe ya tabbatar da cewa a halin yanzu 'yan sanda na kan bincike kuma za a dauki matakin da ya dace da zaran an kammala gudanar da bincike, Daily Post ta rahoto.

Source: Twitter
Budurwa ta mutu a dakin saurayi a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa an tsinci gawar wata budurwa 'yar shekara 24 a gidan saurayinta da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni aun nuna cewa, an tsinci gawar Kelechi Ebubechukwu a dakin saurayin nata ne da ke Gwagwalada, kuma ana kyautata zaton ta mutu ne a ranar Talata.
Babu wata alamar rauni ko shan wuya a jikinta, lamarin da ya sa ake kallon cutar ce ta zama sanadin mutuwarta, ba wai kashe ta aka yi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


