Tsautsayi: Tankar Mai Ta Fashe a tsakiyar Mutane Ranar Juma'a, An Rasa Rayuka da Yawa

Tsautsayi: Tankar Mai Ta Fashe a tsakiyar Mutane Ranar Juma'a, An Rasa Rayuka da Yawa

  • Wata tanka makare da man fetur sama da lita 30,000 ta fashe a kan babban titin Abeokuta zuwa Sagamu a jihar Ogun
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama da ba a tantance adadinsu ba sun mutu sakamakon fashewar tankar yau Juma'a
  • Jami'an hukumomin bada agajin gaggawa na ci gaba da kokarin kashe wutar da ta kama bayan faduwar tankar feturin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Wata tankar mai ta fashe kuma ta kama da wuta a babban titin Abeokuta zuwa Sagamu a jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa mummunar gobara ta tashi a tsakiyar jama'a da matafiya, wadanda ke zirga-zirga a kan babban titin kamar yadda aka saba.

Jihar Ogun.
Hoton taswirar jihar Ogun a Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da daddare, wayewar garin yau Juma'a, 3 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Zuwa kotu da abubuwan da ake fada kan takarar Jonathan a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tanka ta yi ajalin mutane a Ogun

Bayanai sun tabbatar da cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a wannan mummunan hatsari, sai dai har yanzu ba a gama tantancin adadin wadanda suka mutu ba.

Mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Juma’a.

Ya ce hatsarin ya afku ne lokacin da wata tanka mai ɗauke da lita 33,000 na fetur ta kife sakamakon gudu fiye da kima, lamarin da ya sa man ya zube a kan babbar hanyar.

Yadda hatsarin tankar ya yi ajalin mutane

Yayin da yake magana da ’yan jarida, Akinbiyi ya ce:

“Mun samu rahoton mummunar gobara da ta tashi sakamakon hatsarin tanka ɗauke da lita 30,000 na fetur, wadda ta faɗi ta zubar da mai a kan titin Abeokuta–Kobape–Siun–Sagamu da misalin ƙarfe 01:00 na yau.

Kara karanta wannan

Fargabar ambaliya: Kainji da manyan madatsu 3 a Najeriya na shirin kwararo ruwa

“Wutar ta kone babbar mota da wata motar da ke ajiye a gefen hanya, sannan ta lalata wani layin wutar lantarki na PHCN da ke kawo wuta zuwa garin Mowe da kewaye.”

Ya ce a halin yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba, domin jami’an ciki har da TRACE, hukumar kashe gobara ta Ogun, hukumar Nestlé PLC, FRSC da ’yan sanda,na ci gaba da kokarin kashe wutar.

Yan kwana kwana.
Jami'an hukumar kashe gobara ta Najeriya a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

An bukaci matafiya su bada hadin kai

Babatunde Akinbiyi ya roƙi jama’a musamman masu amfani da ababen hawa da ke wucewa ta wannan hanya, da su kwantar da hankalinsu, in ji Daily Trust.

Ya bukaci su kasance masu haƙuri kuma su bada haɗin kai ga tsarin zirga-zirga da kuma matakan da hukumar TRACE, ’Yan Sanda, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Ogun, FRSC, Amotekun da NSCDC suka ɗauka.

“Duk wani cikas ko rashin jin daɗi da ya biyo bayan wannan mummunan lamari, muna ba da haƙuri," in ji shi.

Tankar dakon mai ta fashe a Zaria

A wani labarin, kun ji cewa wata tankar mai ta fashe a unguwar Dan Magaji da ke cikin garin Zariya a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Abin Fashewa ya tarwatse a tsakiyar kananan yara a cikin birnin Kano, ya yi barna

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya afku bayan tankar man da wata mota kirar Golf suka yi taho mu gama, lamarin da ya jawo kara mai tsanani.

Shaidun gani da iso sun bayyana cewa wani hayaki mai kauri ya turnuke saman inda tankar ta ke, abin da ya sa jama’a suka rika gudu domin tsira da rayukansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262