Sauki Ya Zo: Talakawa Za Su Huta, Dokar Lantarki Za Ta Rage Musu Tsadar Wuta

Sauki Ya Zo: Talakawa Za Su Huta, Dokar Lantarki Za Ta Rage Musu Tsadar Wuta

  • Shugaban hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya, NERC, Abdullahi Ramat ya yi albshir ga talawan kasa
  • Ramat ya bayyana cewa talakawa, makarantu da asibitoci za su amfana da rangwamen kuɗin wuta ƙarƙashin dokar wuta ta 2023
  • An kafa wani tsarin tallafin wuta domin rage wa marasa galihu da muhimman cibiyoyi nauyin hauhawar kuɗin wuta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano – Sabon shugaban hukumar kula da harkokin lantarki ta Najeriya (NERC), Abdullahi Ramat, ya bayyana sauki da talakawa za su samu.

Ramat ya bayyana cewa talakawa, makarantu da asibitoci za su samu rangwamen kuɗin wuta ƙarƙashin dokar lantarki ta shekarar 2023.

Za a samu rangwamen tsadar wuta a Najeriya
Shugaban kasa, Bola Tinubu da shugaban NERC a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Engr Abdullahi Garba Ramat.
Source: Facebook

Za a samu sauki wutar lantarki a Najeriya

Ramat ya bayyana hakan ne a Kano lokacin da ya karɓi tawagar asibitin koyarwa ta Aminu Kano, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fara binciken Ganduje, an jero zunuban da ake tuhumarsa da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar ya ce hukumar za ta aiwatar da tsarin tallafi na wuta (PCAF) domin rage nauyin hauhawar kuɗin wuta ga marasa galihu da muhimman cibiyoyi.

An kafa asusun ne ta hanyar dokar lantarki domin tallafawa talakawa wajen biyan kuɗin wuta, tare da tallafa wa makarantu da asibitoci.

Za a rika samun kuɗin daga kasafin gwamnatin tarayya da kuma gudunmawar manyan masu amfani da wuta.

Gwamnati za ta samar da sauki kan biyan wutar lantarki
Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu. Hoto: Adebayo Adelabu.
Source: Twitter

Yadda tsarin tallafin wuta zai yi aiki

NERC ce za ta kula da gudanar da asusun, tana bibiyar yadda ake tara kuɗaɗe da kuma yadda ake raba su.

A cewar dokar, duk wani kamfani ko mutum da ya gaza biyan kudin da aka ware masa zai fuskanci tara mai tsanani.

Ramat ya bayyana cewa manufar ita ce kare talakawa da muhimman cibiyoyi daga tashin kuɗin wuta, tare da tabbatar da kasuwa mai gaskiya da adalci.

Ya kara da cewa, wannan shiri ya yi daidai da burin gwamnati na tabbatar da dorewar samar da wuta mai arha a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jonathan ya ce Boko Haram ta taba zabar marigayi Buhari a matsayin wakili

“Na karɓi bakuncin Farfesa Abdurrahman Sheshe, Babban Darakta na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano tare da dukan tawagarsa a gidana nan Kano.
"Mun tattauna yadda za a tabbatar da wuta mai dorewa da kuma samun sauki wurin biyan kudin wutan ga asibitin.
"Na kuma bayyana shirin hukumar NERC na ƙaddamar da tsarin tallafin wuta (PCAF) ƙarƙashin dokar wuta ta 2023, wanda zai rage nauyin kuɗin wuta ga makarantu, asibitoci da talakawa masu ƙaramin karfi.”
“Wajibi ne mu kare hakkin masu amfani da wuta tare da tabbatar da cewa masu saka hannun jari sun samu kwarin gwiwa."

- Abdullahi Ramat

Ma'aikacin wuta ya tattauna da Legit Hausa

Daya daga cikin ma'aikata a kamfanin JED ya ce tabbas matakin zai taimaka.

Aliyu Adam ya ce:

"Muna shan wahala wurin karbar kudin wuta daga mutane saboda tsadar wuta da kuma yadda wasu yankuna ba su samunta."

Adam ya ce tallafin zai taimaka wurin saukaka musu da kuma su kansu talakawa.

Gwamnati ta cimma yarjejeniya da ma'aikatan wuta

A wani labarin, an dakatar da yajin aikin ma’aikatan wutar lantarki bayan sa’o’i 10, wanda ya hana fuskantar matsanancin rashin wuta.

Kara karanta wannan

Tazarce: An zakulo manyan abubuwa 6 da za su taimaka wa Tinubu ya ci zabe a 2027

Ma’aikata da gwamnatin tarayya sun cimma yarjejeniya a wani taron gaggawa da aka gudanar a Abuja bayan barazanar ma'ikatan.

Kungiyoyin kwadago sun ce sun dakatar da yajin aiki ne amma za su dawo da shi idan gwamnati ko TCN suka saba alkawari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.