Hare Hare da Kona Fadarsa Ya Tilastawa Sarki Tserewa Kamaru, Mutanensa Sun Bi Shi
- Harin yan Boko Haram ya tilasta wa Sarki da wasu daga cikin mutanensa yin hijira zuwa kasar Kamaru
- An ce Sarkin Kirawa, Alhaji Abdulrahman Abubakar, ya tsere zuwa Kamaru bayan Boko Haram sun kona fadarsa
- Rahotanni sun nuna mutane da yawa sun tsere zuwa Kamaru da Maiduguri, yayin da wasu suka je Pulka da sojoji ke zaune
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kirawa, Borno - Mazauna Kirawa a jihar Borno sun ga ta kansu bayan harin yan ta'addan Boko Haram a yankinsu.
Dalilin harin, Sarkin Kirawa a jihar Borno, Alhaji Abdulrahman Abubakar, ya tsere zuwa kasar Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya.

Source: Facebook
Rahoton Punch ya ce basaraken ya dauki matakin ne bayan ’yan ta’adda sun kona fadarsa a wani hari da suka kai a wannan mako.

Kara karanta wannan
An rage mugun iri: Sojojin sun sada hatsabibin dan bindiga da yaransa da mahaliccinsu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin Boko Haram da ya rikita mutanen Kirawa
Wannan mataki na Sarkin ya biyo bayan hare-haren yan kungiyar Boko Haram da ya yi kamari a yankinsa da ke jihar Borno.
Yayin harin, miyagu sun hallaka mutum daya tare da kona gidaje da shaguna na mutanen garin Kirawa da ke karamar hukumar Gwoza.
Sanata Ali Ndume wanda yankin ke karkashin wakilcinsa ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya bukaci gwamnati ta kara tura jami'an tsaro zuwa yankin.
Yadda mazauna Kirawa ke tserewa a gidajensu
Mazauna garin sun bar gidajensu da dama, wasu sun shiga manyan motoci zuwa Kamaru, yayin da wasu suka tsere zuwa Maiduguri da Pulka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Kirawa ta zama kufai, bayan gidaje da dama da fadar Sarki sun kone a harin da ’yan ta’adda suka kai.
Shugaban Kungiyar Cigaban Kirawa, Yakubu Mabba Ali, ya roki gwamnati da ta kafa sabuwar rundunar soji domin tsaron iyakar yankin.

Source: Original
An tabbatar da tserewar Sarki zuwa kasar Kamaru
Wani da ya tsere zuwa Maiduguri, Aji Modu ya ce kowa ya bar garin, hatta Sarkin yanzu yana kwana a Kerawa ta Kamaru.
Ya bayyana cewa kaso 60 cikin ɗari na jama’a sun tsere zuwa Kamaru, sauran kuma sun watse a kauyukan Borno da Maiduguri.
Wani mazaunin yankin, Atahiru Lawan, ya bayyana cewa suna tsoron karin hari da sojojin Kamaru suka bar garin bayan rikici ya ɓarke.
Sanata Ali Ndume ya nuna damuwa kan harin, inda ya ce rashin sojoji a Kirawa ya haddasa faruwar lamarin, inda aka kai wa farauta da JTF harin kwantan bauna.
Ya bayyana cewa ’yan Boko Haram sun kashe ɗan sa kai guda, suka ƙone motoci guda shida, ciki har da Golf biyu da babbar motar haya.
Yadda sojoji suka tsere bayan harin Boko Haram
Mun ba ku labarin cewa yan ta'adda dauke da makamai sun yi ta'asa bayan kai wani harin ta'addanci a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.
Harin ya jawo an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin 'yan ta'addan da dakarun sojoji, wadda ta dauki dogon lokaci.
Daga baya, 'yan ta'addan sun kwashe makamai a sansanin sojoji bayan jami'an tsaro sun ja da baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

