Yadda Sakon WhatsApp Ya Jawo Matatar Dangote Ta Kori Ma'aikata 800
- Yayin da rikicin kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta PENGASSAN da Matatar Dangote ke zuwa karshe, an gano asalin rigimar
- Wata majiya ta bayyana cewa matatar ta kori wasu daga cikin ma'aikatanta ne bayan PENGASSAN ta saka su a wani zaure na WhatsApp
- An gano cewa jagororin kungiyar ta PENGASSAN ta nemi ma'aikatan da ke cikin kungiyar su rika miko mata bayanan ayyukan matatar a kullum
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – An gano dalilin da ya jawo matatar Dangote ta dauki matakin korar wasu daga cikin ma'aikatanta guda 800.
Rikici ya kaure a tsakanin matatar Dangote da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasa, PENGASSAN saboda zargin raba ma'aikata da hanyar samun abincinsu.

Source: Getty Images
Amma wata majiya ta shaidawa jaridar Premium Times cewa PENGASSAN ta bude wani zaure a kafar Wwhatsapp, wanda haka ya jawo korar ma'aikatan.
Dalilin korar 'yan PENGASSAN daga matatar Dangote
Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan 'yan kungiyar PENGASSAN sun tuntubi wasu ma’aikatan matatar, suna gayyatarsu shiga ƙungiyar da alkawarin ba su kariya.
An gano cewa ta cikin shafin da PENGASSAN ta bude, an bayar da takardun rijista da kungiya kuma neman wasu rahotannin sirri a kan ayyukan matatar.

Source: Getty Images
Majiyoyin sun bayyana cewa matatar Dangote ta dauki neman fitar da bayanan ayyukanta a matsayin babbar barazana da kuma cin amana daga bangaren ma'aikatanta.
Rahotanni sun bayyana cewa duk da korar da aka yi na da nasaba da sake fasalin tsarin aiki gaba ɗaya, amma fitar da bayanan kamfanin ya kara ta'azzara lamarin.
Yadda matatar Dangote ta kori ma'aikata
Wata wasika da babban manajan kula da ma’aikatan kamfanonin Dangote, Femi Adekunle, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa daga ranar 25 ga Satumba, 2025 an sallami ma'aikatan kan zargin cin amana.
Bayan korar ma’aikatan, PENGASSAN ta nemi dakatar da isar da iskar gas zuwa matatar, tare da umartar 'ya'yanta a fadin ƙasa da su janye ayyukansu a fadin kasar nan.
Sai dai, Matatar Dangote ta bayyana umarnin PENGASSAN a matsayin ba bisa ƙa’ida ba, tare da kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su shigo cikin lamarin.
A ranar Litinin, kotun masana’antu ta ƙasa a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da yajin aikin da kuma hana katse iskar gas daga isa matatar.
A ranar Laraba, PENGASSAN da matatar Dangote su ka cimma yarjejeniya bayan tawagar gwamnatin tarayya ta shafe kwanaki ana shiga tsakani.
An cimma matsaya tsakanin Dangote da PENGASSAN
A baya, mun wallafa cewa bayan kwana biyu ana tattaunawa a tsakanin Matatar Dangote da ƙungiyar PENGASSAN, gwamnatin tarayya ta yi nasarar warware rikicin bangarorin biyu.
Ministan Kwadago, Maigari Dingyadi ya bayyana cewa an yi doguwar tattaunawa kafin a cimma daidaito a tsakanin Dangote da ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas wato PENGASSAN.
Rahotanni sun ce ɓangarorin biyu sun amince da wasu muhimman matakai da suka shafi hakkokin ma’aikata da tsaron ayyukansu da kuma janye yajin aikin da PENGASSAN ta shiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

