Yadda Jami'an Tsaro Suka Hallaka Tantirin Dan Ta'adda a Kwara
- Jami'an tsaro sun samu nasarar rage mugun iri ta hanyar hallaka daga cikin manyan 'yan ta'addan da ke addabar mutane a jihar Kwara
- Masu aikin samar da tsaron sun hallaka hatsabibin dan ta'addan ne mai suna Maidawa a karamar hukumar Isin
- Hakazalika, jami'an taaron sun hallaka abokan aikinsa bayan an yi musayar mai zafi tsakanin bangarorin biyu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka wani hatsabibin dan ta'adda kuma sanannen mai garkuwa da mutane, Maidawa, a jihar Kwara.
Jami'an tsaron sun hallaka Maidawa ne tare da wasu daga cikin abokan aikinsa bayan artabun da suka yi a garin Isanlu, karamar hukumar Isin, a karshen mako.

Source: Facebook
'Jami'an tsaro sun kashe dan ta'adda
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
An rage mugun iri: Sojojin sun sada hatsabibin dan bindiga da yaransa da mahaliccinsu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, bayanan sadarwa da hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta saurara sun nuna cewa an kashe Maidawa da abokan aikinsa a yayin samamen da aka kai a kan iyakar jihohin Kwara da Kogi.
Rahotanni sun nuna cewa, wani shahararren mai garkuwa da mutane da aka dade ana nema, Baccujo, ne ya sanar da sauran ‘yan tawagarsu, labarin mutuwar Maidawa.
Ya sanar da su labarin mutuwar ne lokacin da yake kan hanyar Igboro–Idofin, yayin da yake magana da abokan aikinsa a Marabar Maigora, karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.
Hukumomi na kai hare-hare kan 'yan ta'adda
Hukumomi sun bayyana cewa jami'an tsaro sun kara kaimi wajen kai samamen ne, bayan sabon umarnin da gwamnatin jihar ta bayar, domin shawo kan matsalar garkuwa da mutane da ke addabar al’umma a yankin.
Jami’an tsaro sun yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kakkabe ‘yan ta’adda a matakai daban-daban a cikin kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Edu, da Patigi.
Za su ci gaba da kai samame kan 'yan ta'addan ne domin rusa kungiyoyin masu laifi da kuma hana ci gaba da sace mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka.

Source: Original
Karanta karin wasu labaran kan 'yan bindiga
- Bulama Bukarti ya hango matsaloli a sulhu da ƴan ta'adda, ya ba gwamnati shawara
- An hallaka shedanin dan bindiga, matasa sun kona fadar Sarki da harsashi ya samu dalibai
- DSS sun kwace makaman yan sa kai kafin harin yan bindiga? Gwamnati ta magantu
- Shiga sharo ba shanu: Yan ta'addan Lakurawa sun hallaka mata kan zargin maita
'Yan bindiga sun sace malamar asibiti
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da wata malamar asibiti mai suna, Rad. Basheerah Ojedeyi, a jihar Neja.
'Yan bindigan sun sace malamat asibitin ne lokacin da take kan hanyar komawa gidansu da ke jihar Osun, bayan kammala bikin rantsuwar kama aiki.
Tsagerun sun kuma bukaci a ba su miliyoyin kudade da suka kai N2m kafin su sako matashiyar malamar asibitin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
