'Za Ki Warke': An Kama Malamin Addini kan Zargin Kwanciya da Budurwa na Kwana 7

'Za Ki Warke': An Kama Malamin Addini kan Zargin Kwanciya da Budurwa na Kwana 7

  • Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani malamin addinin Kirista da ya rutsa budurwa, yake yin lalata da ita na tsawon lokaci
  • Jami'an yan sanda a jihar Ebonyi ta kama limamin coci, Fasto Ndibueze Okorie, bisa zargin aukawa marar lafiya mai cutar sikila
  • Wani bidiyo ta nuna yarinyar ta bayyana cewa Faston ya yaudare ta da cewa jima’i na tsawon kwana bakwai zai canja tsarin halittarta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Rundunar ‘yan sanda a jihar Ebonyi ta yi ram da wani malamin coci kan yaudarar wata mai cutar sikila

Rundunar ya kama shugaban coci, Fasto Ndibueze Onyagoziri Okorie, bisa zargin yin jima’i da wata marar lafiya.

Yan sanda sun kama fasto kan zargin kwanciya da budurwa a Ebonyi
Babban sufeta-janar na yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Yan sanda sun kama Fasto kan tarewa da marar lafiya

Kakakin rundunar, SP Joshua Ukandu, shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a yau Alhamis 2 ga watan Oktoba, 2025, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Yadda wani shugaban APC ya mutu yana cikin raba N50,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ukandu ga tabbatar da cewa Faston yana hannunsu tun daga ranar 1 ga Oktoba 2025 yayin da ake ci gaba da bincike.

“Eh, Faston yana hannunmu, ana bincikensa domin tabbatar da gaskiyar lamarin, Wannan shi ne abin da zan iya faɗi yanzu.”

- Joshua Ukandu

Abin da budurwar ta ce game da Faston

A bidiyo da ya yadu, yarinyar mai shekara 22 ta ce ta koma zama tare da limamin saboda yanayin cutar sikila da take fama da shi.

Ta bayyana cewa Faston ya ce kwanaki bakwai na jima’i tsakaninsu zai sauya tsarin halittarta daga daga SS zuwa AA, amma hakan bai faru ba.

Matar ta ce saboda wahalar cutar da ta riga ta kashe ‘yan uwanta, ta amince da shawarar, amma daga baya matsalolin lafiyarta suka tsananta.

Fasto ya shiga hannu kan zargin kwanciya da budurwa
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Barazanar da Faston ya yiwa budurwa

Bayan ta sanar da ‘yar uwarta, sai aka tilasta mata ta koma gida, inda Faston ya fara barazanar wallafa hotunanta tsirara idan ta gudu.

Kara karanta wannan

Abin kunya: Malamin addini ya yaudari yar'uwa da ƙanwarta a wurin ibada, ya auka musu

Rahoton Leadership ya ce budurwar ta ga hotunanta tsirara tare da Faston sun bayyana a shafukan sada zumunta, lamarin da ya tayar da muhawara sosai.

Sai dai Faston ya musanta zargin gaba ɗaya, inda ya ce ba shi ya yi jima’in ba, kuma an yi amfani da manhajar AI bayan satar wayarsa.

A halin yanzu, yarinyar da take korafin ta ce a cikin wata hira da ta yi da ’yan jarida cewa Faston ne ya ɗauki hotunan tun lokacin da take zaune a gidansa tun daga 2021.

Hukumomin ’yan sanda sun bayyana cewa bincike yana ci gaba domin gano hakikanin gaskiyar da ke tattare da lamarin.

Ana zargin Fasto da aukawa yar'uwa da kanwarta

A baya, mun ba ku labarin cewa dubun wani malamin addinin Kirista ya cika bayan cafke shi da cin amana yayin wa'azi a cocinsa.

An tura Faston mai shekara 63, Luke Eze, gidan yari bayan an tuhume shi da cin zarafin ’yan mata biyu a Enugu.

Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa ya yaudari yaran masu shekara 16 da 19 zuwa coci sannan ya batar musu da hankali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.