Ana Take Su: Sanusi II Ya Faɗi Ƙoƙarin da Ya Yi wurin Tabbatar da Yi Wa Mata Gata

Ana Take Su: Sanusi II Ya Faɗi Ƙoƙarin da Ya Yi wurin Tabbatar da Yi Wa Mata Gata

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ba da shawara kan shigan mata harkokin siyasa a Najeriya
  • Basaraken ya bukaci gwamnati ta cire shinge da ke hana mata shiga siyasa, kasuwanci da shugabanci
  • Sanusi II ya bayyana yadda ya kawo sauyi lokacin da yake gwamnan babban bankin Najeriya, CBN

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci daukar matakai na musamman domin kawo sauyi game da rayuwar mata.

Sarkin ya bukaci cire tsaiko da ke hana mata shiga siyasa, kasuwanci da shugabanci a Najeriya.

Sanusi II ya bukaci cusa mata a siyasa da kasuwanci
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yayin rangadi a Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Twitter

Sanusi II ya bukaci ba mata dama

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya yi wannan jawabi ne a wani taro da aka gudanar a Lagos, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi ya bayyana cewa karfafa daidaiton jinsi a harkar kudi zai kawo ci gaba mai girma, yana mai cewa lamarin ba taimako ba ne.

Kara karanta wannan

"Ku daina": Tinubu ya yi nasiha ga 'yan Najeriya kan wata mummunar dabi'a

Ya kara da cewa an yi wasu shingaye da ake dangantawa da mata a shugabanci ne da gangan, domin hana su samun dama da wakilci.

Sanusi II ya ce:

“Me ya sa dokar kasa ba ta ce kashi 30 cikin 100 na ministoci su kasance mata ba? Me ya sa bambancin kawai a yankunan jihohi ne?”

Sanusi II ya ce Najeriya na da Sanatoci 109 amma mata hudu kacal ne a cikinsu wanda abin takaici ne.

Ya ba da shawarar a rika ware kujerar Sanata daya a kowace jiha ga mata domin samun daidaito da wakilci nagari.

Sanusi ya tuna cewa lokacin da ya zama gwamnan CBN a 2009, mata hudu kacal suka taba zama darakta tun daga 1959.

Sarki Sanusi II ya goyi bayan ba mata dama a iyasa
Sarki Muhammadu Sanusi II a fadarsa da ke Kano. Hoto: @masarautarkano.
Source: Twitter

Sauye-sauye da Sanusi ya kawo a CBN

A cewarsa, bankin ya rage sharuddan daukar matsayin darekta daga shekaru uku zuwa shekara daya domin bunkasa damar mata a mukaman jagoranci.

Sanusi ya bayyana yadda ya nada mata shugabanni a muhimman sassa kamar wajen sa ido kan bankuna, kula da hadari, lissafi da kuma gudanar da rassan banki.

Kara karanta wannan

Abba ya jero bangarori 5 da gwamnatin Kano ta farfado da su a cikin shekaru 2

Ya ce nasarorin da aka samu a lokacin nasa sun samo asali ne daga bajintar mata da shugabancin da suka bayar a wuraren ayyuka, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Bisa wannan tsari, bankuna suka fara daukar matakai, wanda ya kai ga shekara ta 2012 da aka bayyana a matsayin “Shekarar Mata a Bankuna.”

Ya ce daga baya bankuna tara aka samu shugabancin su ya koma hannun mata, alamar ci gaba a bangaren shugabancin mata.

Sanusi II ya ce sauye-sauyen wurin aiki irin su karin hutu ga masu juna biyu da damar aiki daga gida sun tabbatar da dorewa bayan annobar COVID-19.

Sanusi II ya magantu kan cire tallafi

Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan yadda ake samun lalatattun shugabanni a Najeriya.

Basaraken ya ce kasar ta dade tana fama da shugabanni marasa inganci, lamarin da ya hana cigaba sosai.

Sanusi II ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya ceci kasar daga durkushewa, yana mai ba matasa shawara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.