Abin Fashewa Ya Tarwatse a tsakiyar Kananan Yara a cikin Birnin Kano, Ya Yi Barna

Abin Fashewa Ya Tarwatse a tsakiyar Kananan Yara a cikin Birnin Kano, Ya Yi Barna

  • Wasu kananan yara sun dauko kwalbar hayaki mai sa hawaye daga bola ba tare da sun sani ba a jihar Kano
  • Kwalbar ta fashe kuma ta jikkata mutum hudu yan gida daya a unguwar Bakin Kwata a Sharada da ke cikin birnin Kano
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun killace wurin da bolar da yaran suka dauko kwalbar domin gudanar da bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Kwalbar barkonon tsohuwa mai sanya hawaye wadda 'yan sanda ke amfani da ita ta tarwatse a cikin mutane a jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa yara hudu yan gida daya sun ji raunuka sakamakon fashewar kwalbar a unguwar Bakin Kwata da ke Sharada a cikin Kano.

Taswirar jihar Kano
Hoton taswirar jihar Kano. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ne ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

DSS sun kwace makaman yan sa kai kafin harin yan bindiga? Gwamnati ta magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:50 na safiyar ranar Laraba.

Abin da ya faru bayan fashewar kwalbar

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce fashewar ta haifar da hayaki mai yawa, zafi a jiki da kuma matsanancin ƙamshi mai hana mutane numfashi.

Wannna lamari ya sa dakarun sashen kwararru masu kwance bam a rundunar yan sanda suka killace yankin domin tabbatar da tsaro da kuma gudanar da binciken bayan fashewar.

Yara hudu sun jikkata a Kano

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Khadeeja Rabiu mai shekaru 17, ta ji mummunan rauni a hannunta na dama da wasu sassan jikinta.

Sauran ’yan uwanta Fatima (15), Alamin (11), da Suleiman (3) sum samu raunuka kaɗan. Dukkaninsu an garzaya da su zuwa Asibitin Murtala Muhammed domin yi masu magani.

A yayin bincike, ’yan sanda sun gano hannun kwalbar, mabudi da murfinta, inda aka ce har yanzu hayakin barkono yana fitowa daga ciki.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane

'Yan sandan Kano sun gudanar da bincike

Binciken ya gano cewa yara ne suka dauko kwalbar a wata bola da ke kusa, kuma ɗaya daga cikin yaran ya taho da ita gida, daga bisani ta fashe a hannun Khadeeja.

Jami'an tsaro sun ce su na ci gaba da tantance bolar don gano ko akwai wasu kayayyaki masu haɗari, tare da wayar da kan al’umma kan haɗarin ɗaukar abubuwan da ba a sani ba daga wuraren zubar da shara.

An kama masu laifi sama da 100 a Kano

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yaki da laifuffuka a watan Satumban 2025.

Rundunar ta ce wannan nasarori sun samu ne karkashin Operation Kukan Kura, wanda ta kirkiro da nufin kakkabe miyagun laifuka da daba a jihar Kano.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Bakori ya ce an samu raguwar laifuffuka tare da kama mutane 105 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka a watan Satumba kadai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262