An Yi Baban Rashi: Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Sa'id Abubakar Ya Rasu a Kaduna
- Babban limamin masallacin Juma'a na SMC da ke garin Kaduna, Sheikh Imam Sa'id Abubakar ya rasu da safiyar yau Alhamis, 2 ga Oktoba, 2025
- Majalisar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna ta tabbatar da rasuwar malamin a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ya cika ne da asubah
- Tuni dai aka yi jana'izar marigayin da misalin karfe 1:00 na rana bayan Sallar Azahar kamar yadda addinin musulunci ya tanada
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Babban Malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, Sheikh Imam Sa'id Abubakar ya riga mu gidan gaskiya.
Majalisar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna ta tabbatar da rasuwar Imam Sa'id, ta ce ya rasu ne da Asubahin yau Alhamis, 2 ga watan Oktoba, 2025.

Source: Facebook
An tabbatar da rasuwar Sheikh Sa'id Abubakar

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
Sakataren Majalisar Limamai da Malamai ta Kaduna, Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa shafinsa na Facebook.
Ya ce Marigayi Imam Sa'id Abubakar shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Sardauna Memorial College watau SMC da ke Unguwan Dosa a cikin garin Kaduna.
Sanarwar ta ce:
"Inna lillahi wa inna Ilaihi Raji'un. Majlisar Limamai da Malamai na Jihar Kaduna na sanar da cewa Allah Ta'ala ya yi wa Shaikh Imam Sa'id Abubakar rasuwa.
''Marigayin, wanda shi ne babban limamin masallacin juma'a na SMC ya rasu da Asubah yau 10 ga watan Rabi'ul Thani, 1447AH wanda ya zo daidai da 2 ga watan Oktoba, 2025.
"Za'a yi jana'izar shi da karfe 1:00 na tsakar rana bayan Azahar in shaa Allahu. Allah Ya ji ƙan Imam Sa'id Abubakar."
Malamin ya sha fama da rashin lafiya
Bayanai daga Unguwan Dosa a Kaduna sun nuna cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya.
Tuni dai mabiya da sauran mutane suka fara tururuwar zuwa ta'aziyya da alhinin wannan babban rashi da suka yi.
Wani mazaunin Kaduna, Isma'il Usman ya shaida wa Legit Hausa cewa rashin limaminbabban rashi ne ga musulunci, al'ummar Unguwar Dosa, Kaduna da ma Najeriya baki daya.

Source: Facebook
Mutane sun yi jimamin rashin Imam Sa'id
Ya yi addu'ar Allah ya jikan malamin, Ya amshi kyawawan ayyukansa, kuma Ya sanya shi a gidan aljannah.
"Mun tashi da safiyar yau Alhamis da labarin rasuwar babban malami, Sheikh Sa'id Abubakar SMC (Babban Limamin Masallacin SMC Unguwan Dosa Kaduna."
"Ya rasu ne bayan doguwar jinya da ya yi, Allah Ka jikan Imam Sa'id SMC Ka sa Aljannace makoma, Sheikh Sa'id aminin mahaifina ne sosai," in ji shi.
Malaman darikan Tijjaniya 2 sun rasu
A wani labarin, kun ji cewa manyan malaman Darikar Tijjaniya guda biyu sun riga mu gidan gaskiya a Najeriya.
Malaman da suka rasu su ne Khalifan Tijjaniyya na Jihar Osun, Sheikh Abdul Kareem Raji, da Khalifan Tijjaniyya na Jihar Kwara, Sheikh Abubakar Siddeeq Agbade Abayawo.
Gwamna Ademola Adeleke, ya bayyana bakin cikinsa tare da mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar wadannan manyan malamai na addinin musulunci guda biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
