NNPCL Ya Bayyana Asarar da Aka Tafka sakamakon Yajin Aikin PENGASSAN

NNPCL Ya Bayyana Asarar da Aka Tafka sakamakon Yajin Aikin PENGASSAN

  • Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya haska illar da yajin aikin kungiyar PENGASSAN ya jawo
  • Bayo Ojulari ya bayyana cewa yajin aikin ya jawo asara mai girma a fannin hakar man fetur, iskar gas da samar da wutar lantarki
  • Shugaban na NNPCL ya koka kan cewa idan yajin aikin ya ci gaba, zai yi gagarumar illa ga fannin makamashin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bashir Ojulari, ya yi magana kan yajin aikin da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur na kasa (PENGASSAN) ta gudanar.

Bayo Ojulari ya koka kan asarar da aka yi a fannin hakar mai da iskar gas sakamakon yajin aikin na kwana uku da kungiyar (PENGASSAN) ta gudanar.

Ojulari ya koka kan yajin aikin PENGASSAN
Shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Bayo Ojulari. Hoto: @nnpclimited
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da Ojulari ya rubuta zuwa ga hukumomin NMDPRA da NUPRC.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jonathan ya aika da muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Ojulari ya tura wasika kan yajin aikin PENGASSAN

Ojulari ya bayyana cewa yajin aikin ya haifar da asarar kaso 16 cikin 100 a fannin hakar mai da kashi 30 cikin 100 na iskar gas da ake kasuwanci da shi, tare da janyo ragin kaso 20 cikin 100 na wutar lantarki a kasa.

Wasikar mai dauke da kwanan watan 29 ga Satumba, 2025, an kuma aika ta ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da kuma daraktan hukumar DSS.

Yajin aikin, wanda rikici tsakanin ƙungiyar PENGASSAN da matatar man Dangote ya haddasa, ya tilasta a rufe manyan tashoshin mai, tasoshin iskar gas da wuraren samar da wutar lantarki.

Lamarin ya jawo jinkirin fitar da ganga 283,000 ta man fetur da biliyan 1.7 na iskar gas a kullum.

Hakan ya kawo cikas a muhimman hanyoyin samun kuɗaɗen shiga guda biyu na Najeriya.

Wace irin asara yajin aikin ya jawo?

Kara karanta wannan

PEGASSAN vs Dangote: An rufe gidajen mai, an samu raguwar karfin wutar lantarki

A cikin wasikar, Ojulari ya ce yajin aikin ya haddasa gagarumar asara tun a cikin sa’o’i 24 na farko.

Ya bayyana cewa, a ranar 29 ga Satumba, 2025, an gaza hako ganga 283,000 ta man fetur, iskar gas biliyan 1.7 da rasa samar da fiye da 1,200 megawatts na wutar lantarki.

Yajin aikin PENGASSAN ya jawo asara a Najeriya
Bashir Bayo Ojulari na jawabi a wajen taro. Hoto: @nnpclimited
Source: Twitter
“Wannan yana nufin an rasa kusan kaso 16 cikin 100 na man fetur, kashi 30 cikin 100 na iskar gas da ake kasuwanci da shi, da kuma kashi 20 cikin 100 na wutar lantarki."
"Idan aka ci gaba da wannan yajin aiki, illolinsa za su karu matuka, kuma hakan zai zama babban barazana ga tsaron makamashi na kasa."

- Bayo Ojulari

NNPCL ya samu ribar tiriliyan 1.7

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), ya samu ribar Naira tiriliyan 1.7 sakamakon yarjejeniyar PSC.

Sabon rahoton da kwamitin asusun FAAC ya fitar, ya nuna cewa an samu kudaden a tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2025.

Sai dai, rahoton ya bayyana cewa kamfanin na NNPCL bai tura ko sisi ba a asusun tarayya, duk da wannan ribar da aka samu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng