Gwamnatin Tinubu Ta Yi Martani kan Zargin Jefa 'Yan Najeriya Miliyan 15 a Bakin Cikin Talauci
- Fadar Shugaban Kasa ya musanta ikirarin tsohon 'dan takarar shugaban kasa Peter Obi a kan karuwar talauci a fadin Najeriya
- Tsohon 'dan takarar a jam'iyyar LP, Obi ya ce manufofin Shugaba Bola Tinubu sun sa mutane miliyan 15 shiga matsanancin talauci
- A martaninsa, Bayo Onanuga, babban mai ba Shugaban Kasa shawara a kafafen yada labarai ya ce Obi ya fara tuhumar kansa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Bayo Onanuga, babban mai ba Shugaba Tinubu shawara kan yada labarau, ya yi tir da ikirarin da Peter Obi a kan talauci a Najeriya.
Tsohon 'dan takarar Shugaban kasa, Obi ya yi zargin cewa manufofin gwamnatin APC sun tsananta talauci a kasar, inda jama'a da jama'a su ka dulmiya a talauci.

Source: Facebook
A hira da ya yi da Jaridar Punch, Onanuga ya bayyana cewa maganganun Obi ba su da tushe ballantana makama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta yi watsi da kalaman Obi
Onanuga ya bayyana cewa Peter Obi bai yi la'akari da jawabin Shugaba Tinubu na ranar 1 ga Oktoba ba, da ya fahimci abubuwa da dama a kan halin da kasa ke ciki.
Ya bayyana cewa Tinubu ya jaddada yadda ya gaji kalubalen tattalin arziki daga gwamnatin baya, amma ba a wannan gwamnati aka same su ba.
Ya ce:
“Maganar Obi ba ta kan hanya, kawai yana son wasa da hankalin jama’a ne domin ya samu yabo."
Onanuga ya kara da cewa Obi bai yi cikakken nazari ba, ya kuma kalubalanci tsohon gwamnan kan yadda ya gudanar da jihar Anambra a lokacin mulkinsa.

Source: Facebook
A kalaman hadimin Shugaban Kasa, Obi ya jefa jama'ar jiharsa a cikin talauci fiye da gwamnatocin baya da su ka mulki Anambra.
Ya kuma kara da cewa matsalolin tattalin arzikin Najeriya sun samo asali ne daga shekaru masu yawa na mulkin PDP, ba daga gwamnatin yanzu ba.
Jawabin Onanuga na zuwa ne a lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke cewa gwamnatinsa na aiku tukuru wajen dora tattalin arziki a kan saiti.
Shugaban ya tunatar da cewa a lokacin da ya karbu mulkin Najeriya, tattalin arzikinta yana cikin tsaka mai wuya.
Sau dai a cewar Tinubu, al'amura sun fara daukar harama wajen farfadowar tattalin arzikin saboda sababbin manufofi da gwamnatinsa ta zo da su.
Dattijon Arewa ya yabi mulkin Tinubu
A baya, mun wallafa cewa fitaccen tsohon 'dan siyasa a Najeriya, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa duk wanda ya rayu a lokacin mulkin mallaka ya san kasar nan ta ci gaba.
Ya bayyana cewa Shugabanni kamar su Bola Ahmed Tinubu suna iya bakin kokarinsu wajen ganin Najeriya ta kai ga ci, kuma an samu yalwa mai dore wa a tsakanin al'umma.
A cewarsa, wannan ce ta sa ya ke kara nuna goyon bayansa ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda ya jaddada cewa manufofin gwamnati sun fara kawo sauki ga jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

