Kwankwaso Ya Ziyarci Jagoran Darika, Sharif Saleh bayan an Masa Mutuwa

Kwankwaso Ya Ziyarci Jagoran Darika, Sharif Saleh bayan an Masa Mutuwa

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen malamin addini Sheikh Sharif Saleh a Abuja kan rasuwar ɗansa, Jafar
  • Jagoran NNPP ya samu rakiyar babban jigon jam’iyyar, Buba Galadima, yayin ziyarar ta’aziyyar ranar Laraba 1 ga watan Oktoba, 2025
  • Jama’a da dama sun yi addu’o’i a kafafen sada zumunta suna roƙon Allah ya jikansa ya kuma bai wa iyalan mamacin haƙurin rashin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen malamin addini, Sheikh Sharif Saleh, a Abuja.

Rahoto ya nuna cewa ziyarar ta zo ne sakamakon rasuwar ɗansa mai suna Jafar, wanda ya rasu kwanakin baya.

Kwankwaso a gidan Sheikh Sharif Saleh a Abuja
Kwankwaso a gidan Sheikh Sharif Saleh a Abuja. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a wani sako da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi rashi, jigon tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Sharif Saleh

Kwankwaso ya kai wannan ziyara ne domin nuna tausayinsa a kan babban rashin da Sheikh Sharif ya yi.

Ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa Jafar, ya kuma ba iyalansa da sauran al’umma haƙuri da juriyar rashin.

Kwankwaso ya samu rakiyar babban jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, yayin da suka isa gidan malamin domin yin jaje da addu’ar Allah ya jikan mamacin da rahama.

Sheikh Sharif Saleh da tarihin rayuwarsa

Sheikh Sharif Saleh ne shugaban kwamitin Fatwa na Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya.

An haifi malamin a ranar 12 ga Mayu, 1938 a Aredibe, kusa da karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.

Ya fito daga gidan malamai, inda mahaifinsa Sheikh Muhammad Al-Salih bin Yunus Al-Nawwy ya shahara wajen koyar da ilimin addini.

Sheikh Sharif ya yi karatu a Najeriya da waje, inda ya yi fice a harshen Larabci, Turanci, Hausa da Kanuri.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai yi alaka da Ganduje idan ya koma APC da wasu abubuwa 2

Sanata Rabiu Kwankwaso a wani taro
Sanata Rabiu Kwankwaso a wani taro. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

'Ya'yan Sheikh Sharif Sale da suka rasu

Sheikh Sharif Saleh ya rasa ɗansa Jafar wanda ya rasu a shekarar 2025, abin da ya sa jagororin siyasa da na addini suka yi ta kai masa gaisuwa.

Kwankwaso da Buba Galadima sun kasance cikin waɗanda suka nuna tausayinsu tare da addu’ar Allah ya bai wa iyalan malamin haƙuri.

Sai dai wani rahoto na Daily Trust ya nuna cewa ba wannan ba ne karo na farko da Sheikh Sharif ya fuskanci babban rashi ba.

A shekarar 2023 da ta gabata, ya yi rashin babban ɗansa, Alhaji Musa Alkasim, mai shekara 59, wanda shi ne ɗansa na fari.

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya masa ta’aziyya a lokacin, yana mai kiran marigayin mutum mai amana.

Guruntum ya yi magana kan Triumph

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi tsokaci kan zargin da ake yi wa Sheikh Lawal Abubakar Triumph.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi sun tanka bayan ADC ta ba'yan hadaka umarni

Malamin ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta yi taka tsantsan da tabbatar da adalci kan korafin da aka shigar mata.

Sheikh Guruntum ya kuma yi kira ga masu yi wa Malam Lawan Triumph barazana da su kaucewa daukar doka a hannu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng