Tanko Yakasai Ya Fadi Dalilansa na Goyon bayan Gwamnatin Tinubu

Tanko Yakasai Ya Fadi Dalilansa na Goyon bayan Gwamnatin Tinubu

  • Dattijo kuma tsohon 'dan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa Shugaban Bola Ahmed Tinubu yana bakin kokarinsa
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke bayani a kan irin ci gaban da Najeriya ta samu bayan ta shafe shekaru 65 da 'yancin kai
  • Tanko Yakasai ya ce wandanda su ka yi zamani da Turawan mulkin mallaka za su gane irin matakin ci gaba da Najeriya ta kai a yau

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon ɗan siyasa kuma dattijo, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana cewa Najeriya a yau ta fi yadda take a zamanin kafin samun 'yancin kai.

A kalamansa bayan Najeriya ta cika shekaru 65 da 'yanci daga Turawa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa an Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a tsawon shekarun nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi kira ga 'yan Najeriya a taron da ya hadu da Sanusi II a Legas

Alhaji Tanko Yakasai ya goyi bayan Tinubu
Hotuna daban-daban na Alhaji Tanko Yakasai Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Source: Twitter

Alhaji Tanko Yakasai, wanda yanzu yana da shekaru 99 a duniya, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a tashar Arise TV a shirin The Morning Show a ranar Laraba.

Tanko Yakasai: Na goyi bayan Tinubu

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Alhaji Tanko Yakasai ya jaddada goyon bayansa ga gwamnatin APC a karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu ya samo asali ne daga yadda gwamnati ta nuna aniyyarta ta aiwatar da sauye-sauyen da suka dace.

A cewarsa:

“A ganina, zuwa yanzu, ana iya cewa al’amura na tafiya daidai. Ina ganin mutane da yawa za su yarda da ni cewa Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama tun da ya hau mulki."

Alhaji Yakasai ya ce sai wanda ya san yadda zamanin mulkin mallaka ya kasance zai iya gane irin cigaban da aka samu halin da kasar ke ciki.

Tanko Yakasai yana ganin Najeriya ta ci gaba

Kara karanta wannan

Bayan wuya: Tinubu ya fadi yadda sauki ya fara samu wa Najeriya

Dattijon kuma fitaccen 'dan siyasa a zamaninsa, Alhaji Yakasai ya jaddada cewa samun ikon mulki da ‘yan Najeriya suka yi bayan samun 'yanci shi ne babban ci gaba.

Alhaji Tanko Yakasai ya ce Najeriya ta ci gaba
Hoton Alhaji Tanko Yakasai, tsohon 'dan siyasa a Najeriya Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

Ya ce kafin 1960, Birtaniyya ce ke da iko da dukkanin al’amuran gwamnati a Najeriya, ba kamar yadda ake cin moriya ba a yanzu.

A cewar Alhaji Tanko Yakasai:

“Yanzu babu wani muhimmin mukamin gwamnati da wani Bature ke rike da shi. Duk 'yan Najeriya ne ke da iko da shugabanci, kuma suna iyakar ƙoƙarinsu wajen kyautata kasa."

Game da tsarin zabe kuwa, ya bayyana cewa kodayake tsarin ba cikakke ba ne, amma yana baiwa al’umma damar sauya shugabanni idan ba su yi abin da ake tsammani ba.

A kalamansa:

“Mun ci gaba da gudanar da zaɓe bayan zaɓe. Wadanda suka yi aiki na ci gaba da samun dama, wadanda ba su shirya ba kuma ana maye gurbinsu. Wannan shi ne ci gaba.”

Akpabio ya yi wa Tinubu albishir

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya shirya tarbar gwamnonin jam’iyyun adawa kafin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Taron tsintsiya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi kallon da Tinubu ke yi wa 'yan hadaka

Akpabio ya ce akwai wasu gwamnonin da suka riga suka shirya komawa jam’iyyar APC, kuma ya jaddada cewa ‘yan Najeriya sun fara ganin amfanin manufofin gwamnatin Tinubu.

Sanatan ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da littafi mai taken “Shekaru 10 na jagoranci mai tasiri na gwamnatin APC a Najeriya”, wanda Gwamna Hope Uzodimma na Imo ya wallafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng