Bayan Tinubu Ya Maido Shi Ofis, Fubara Ya Dauki Mataki mai Tsauri a kan Kwamishinoninsa
- Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya fara daukar wasu matakai bayan Shugaba Bola Tinubu ya mayar da shi ofis
- A sabon matakin da ya dauka, Gwamnan ya kori kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati da ke aiki kafin a dakatar da shi
- Gwamna Fubara ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Koli da aka yanke kwanan nan, inda ya bayyana cewa korar ta fara aiki nan take
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya kori dukkanin kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da ke aiki karkashin gwamnatinsa.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Nelson Chukwudi, ya fitar a birnin Fatakwal a daren Laraba ya bayyana cewa wannan mataki ya fara aiki nan take.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa an yi sallamar ne saboda hukuncin kotun koli da ya shafi dukkanin kwamishinonin da sauran jam'an da ya kora.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Ribas ya kori kwamishinoninsa
Premium Times ta ruwaito cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya sallami jami'an gwamnatinsa ne a lokacin bikin ranar 'yancin Najeriya.
Sanarwar da Nelson Chukwudi ya fitar ta ce:
“Gwamna ya sallami dukkanin kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da wannan hukuncin Kotun Koli ya shafa daga mukamansu nan take.”
A cikin jawabinsa a faretin ranar 'yancin kasa, Fubara ya yaba da muhimmancin bikin ’yancin Najeriya, inda ya yi kira ga jama'a da su yi aiki da Shugaba Bola Tinubu don gina kasa.
Gwamna Fubara zai hidimta wa Ribas
Gwamnan ya kara addada aniyarsa ta ci gaba da hidimta wa jihar tare da gode wa jama’a bisa goyon bayansu, sannan ya yi fatan alheri da murnar zagayowar ranar samun ’yancin kasa.

Kara karanta wannan
"Mun ceto Naira," Tinubu ya tabo batun darajar kudin Najeriya a jawabin ranar 'yanci

Source: Facebook
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Mai girma Gwamnan Jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara, ya gode wa 'yan majalisar zartarwarsa bisa hidima da gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar a tsawon shekaru biyu da suka gabata.
A baya, Kantoman riko, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya, ya dakatar da dukkan kwamishinoni, mashawarta na musamman da mataimaka na musamman da Fubara ya nada.
Ibas ya kuma rusa dukkannin kwamitoci da hukumomi tare da dakatar da shugabanninsu. Sai dai bayan ya sauka daga rikon mukamin a ranar 18 ga Satumba aka fara nazarin makomarsu.
Wannan ya faru ne bayan Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya dakatar da Fubara tare da ayyana dokar ta-baci a jihar.
Ribas: Fubara ya nemi afuwar Wike
A baya, mun wallafa cewa Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas ya ziyarci gidan tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, inda ya roƙi yafiya tare da neman sulhu tsakanin su.

Kara karanta wannan
Kwamishinan 'yan sanda ya fusata Gwamna Abba a wurin faretin ranar 'yancin kai a Kano
An ce ziyarar ta biyo bayan tattaunawar da Fubara ya yi da Shugaba Bola Tinubu a London, inda suka tattauna matsalolin siyasar jihar Ribas bayan an dakatar da shi daga aiki.
A lokacin ganawar da ta biyo wacce aka yi a Abuja, rahotanni sun ce Fubara ya rusuna har ƙasa yana rokon Wike ya gafarta masa kura-kuran da ya yi, inda ya kira shi “Oga na.”
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
