Gwamna Uba Sani Ya Kinkimo Aikin da Aka Kwashe Shekara 50 Ana Alkawarin Yi a Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Kinkimo Aikin da Aka Kwashe Shekara 50 Ana Alkawarin Yi a Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya share hawayen mutanen kauyen Danbushiya da ke karamar hukuma Chikun
  • Mutanen yankin sun kwashe shekaru suna fatan za a yi musu aikin da za su ci ribar gwamnati, amma ba a taba cikawa ba
  • Gwamna Uba Swanda bayan hawansa mulki ya fara gudanar da aikin, ya yi alkawarin zai kammala nan da watanni masu zuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani ya cika burin shekaru 50 na al’ummar kauyen Danbushiya da ke Millennium City a karamar hukumar Chikun.

Gwamna Uba Sani ya cika burin ne ta hanyar fara aikin gina hanya mai tsawon kilomita 15 tun bayan hawansa mulki.

An yabawa Gwamna Uba Sani a Kaduna
Gwamna Uba Sani na jawabi a wajen wani taro. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Dagacin Danbushiya, Alhaji Muktar Haruna, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Abba ya jero bangarori 5 da gwamnatin Kano ta farfado da su a cikin shekaru 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uba Sani ya je duba aiki

Alhaji Muktar Haruna ya bayyana hakan ne lokacin da Gwamna Uba Sani ya kai ziyarar duba aikin hanyar Keke–Danbushiya wadda za ta haɗa sama da kauyuka 15.

Dagacin ya ce an dade ana yi wa al’ummar yankin alkawarin gina hanyar tun lokacin mulkin soja, amma burinsu bai cika ba sai da Gwamna Uba Sani ya hau mulki, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar da labarin.

An yabawa aikin gwamnatin Uba Sani

Alhaji Muktar Haruna ya godewa gwamnan bisa kawo musu romon dimokuraɗiyya ta hanyar samar da asibiti, makarantun firamare da sakandare da kuma inganta tsaro.

Ya kara da cewa a halin yanzu ana gudanar da darussa a makarantar sakandare ta kimiyya da Gwamna Uba Sani ya gina a yankin, inda ɗalibai ke ci gaba da karatu.

Ya ce, saboda ƙaunar da gwamnan ya nuna wa al’ummar yankin, suna so a canza sunan Millennium City zuwa Gwamna Uba Sani Millennium City.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda ya fusata Gwamna Abba a wurin faretin ranar 'yancin kai a Kano

Gwamna Uba Sani ya yi jawabi

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Uba Sani ya tuna da cewa tun daga farkon zuwansa kan mulki, ya bayyana cewa zai kokarin ganin kowane yanki ya samu romon dimokuradiyya.

Uba Sani ya samu yabo a Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Ya ce ya zauna tare da al’ummar Danbushiya, ya tattauna da su, inda ya gane cewa wannan hanya tana da matukar muhimmanci domin tana haɗa kauyuka kusan 15.

“A matsayin gwamnati, mun ga cewa yana da matukar muhimmanci mu zuba kuɗi sosai domin tabbatar da gina hanyar kwalta wadda za ta haɗa waɗannan al’ummomi."

- Gwamna Uba Sani

Gwamnan wanda ya yi alkawarin cewa hanyar za a kammala ta a cikin watanni tara, ya yaba wa al’ummar yankin bisa goyon baya da taimakon da suka bai wa dan kwangilar wajen aiwatar da aikin.

Uba ya dauki alkawarin binciken kisan 'yan biki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi magana kan kisan da aka yi wa masu zuwa daurin aure a Plateau.

Kara karanta wannan

Za a shiga kotu da gwamna bayan kisan 'malami' da ya je yi masa wa'azi har gida

Gwamna Uba ya yi alkawarin cewa zai tabbatar an yi adalci ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kisan.

Uba Sani ya jaddada cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa an yi wa mutanen adalci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng