Jerin Tsofaffin Gwamnonin Najeriya 7 da Suka Dawo Manyan Sarakuna
Nadin sarautar tsohon gwamnan Oyo, Oba Rasheed Ladoja a matsayin Sarkin Ibadan ya sanya Legit Hausa nazari kan gwamnonin da suka dawo sarakuna bayan sauka a mulki.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A tarihin masarautun Najeriya, an samu 'yan siyasa da suka rikida zuwa sarakunan gargajiya.
A makon da ya wuce ne aka yi bikin nadin sarautar tsohon gwamnan Oyo, Oba Rasheed Ladoja da aka nada Sarkin Ibadan.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta kawo muku jerin gwamnonin da suka rike mukaman Sarauta bayan sauka daga mulkin siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Sarkin Gwandu ya taba zama gwamna
Sarkin Gwandu, Muhammadu Iliyasu Bashar shi ne gwamnan soja na farko na tsohuwar jihar Gongola, daga 1976-1978, sannan aka sake naɗa shi a 1984.
Muhammadu Iliyasu Bashar ya zama Sarki a shekarar 2005 bayan da aka tsige Alhaji Mustapha Jokolo daga matsayin Sarkin Gwandu na 19.
Jokolo, wanda ya taɓa kasancewa hadimi ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya kalubalanci tsigewar yana mai cewa an yi masa rashin adalci kuma ba a bi tsarin doka ba.
Ya shigar da ƙara a kotu domin a mayar da shi kan karagar mulki, lamarin da ya jawo rikicin shari’a da ya ɗauki kusan shekaru 20.

Source: Facebook
A shekarar 2014, Babbar Kotun Jihar Kebbi ta yanke hukuncin dawo da Jokolo, inda ta bayar da umarnin a mayar da shi, kuma Kotun Ƙoli ta Ƙasa ta tabbatar da wannan hukunci a 2016.
Sai dai Gwamnatin Jihar Kebbi da Sarkin da ke kan karaga yanzu, Alhaji Muhammadu Iliyasu, sun kalubalanci waɗannan hukunci a Kotun Koli.
A ranar 4 ga Yuni, 2025, Kotun Koli ta yanke hukunci, tana goyon bayan Muhammadu Iliyasu bisa cewa Jokolo ya gaza aika sanarwar ƙara ga gwamna kafin fara shari’a
2. Sarkin Suleja ya rike gwamnan Neja
Alhaji Mohammed Awwal Ibrahim, wanda aka haifa a ranar 8 ga Satumba, 1941, shi ne Sarkin Suleja kuma gwamnan farko da aka zaɓa na Jihar Neja a Jamhuriyya ta Biyu ta Najeriya.
A sakon da ya wallafa a X, hadimin shugaba Bola Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz ya lissafa shi a cikin tsofaffin gwamnonin da suka rike sarauta a Najeriya.
A ƙarƙashin jam’iyyar NPN, ya lashe zaɓen gwamna kuma ya yi mulki har zuwa juyin mulkin sojan 1983 wanda Janar Muhammadu Buhari ya hau mulki a dalilinsa.

Source: Facebook
Rayuwarsa ta sauya a shekarar 1993 lokacin da ya zama Sarkin Suleja, sai dai hawa karagar mulkinsa aka tayar da tarzoma, wanda hakan ya kai ga tsige shi a lokacin Sani Abacha a 1994.
Da Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya a 1999, an dawo da shi kan karagar mulki a watan Janairun 2000.
3. Marigayi Sarkin Zuru ya rike gwamna
Mai martaba Sarkin Zuru marigayi Mohammed Sani Sami ya taba rike gwamna a mulkin soja a jihar Bauchi.
Bayan juyin mulkin soja na 31 ga Disamba, 1983 da ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki, an naɗa shi gwamnan Jihar Bauchi.
Ya ci gaba da rike mukamin har zuwa Agusta 1985, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya karɓi mulki daga Buhari.

Source: Facebook
Marigayin ya yi ritaya a shekarar 1990 sannan ya koma garinsu na asali wato Zuru, inda aka naɗa shi Sarkin Zuru.
Major Janar Mohammed Sani Sami ya rasu a birnin London a ranar 16 ga Agusta, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya.
4. Etsu na Bassa Nge tsohon gwamna ne
Abu Ali, wanda yanzu ake kira Abu Ali Mopa III, tsohon Birgediya Janar ne a rundunar sojin Najeriya.
Rahoton Blue Print ya nuna cewa ya rike mukamin gwamnan Jihar Bauchi daga Agustan 1990 zuwa Yuli 1992, a zamanin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida.

Source: Facebook
Yanzu shi ne Etsu na Bassa Nge a Jihar Kogi, abin da ya sanya shi cikin jerin tsofaffin gwamnonin da suka zama sarakuna.
5. Diete-Spiff ya rike sarauta
Rahoton Inter Region ya nuna cewa Alfred Diete-Spiff ne tsohon gwamna na farko da ya zama Sarki a tarihin tarayyar Najeriya.
An haife shi a ranar 30 ga Yuli, 1942, kuma a shekarar 1967, yana da shekaru 24 kacal, aka nada shi gwamnan soja na farko na Jihar Rivers a lokacin yakin basasar Najeriya.
Sai dai aikinsa ya tsaya cak bayan juyin mulkin Janar Murtala Muhammed a shekarar 1975, lokacin da aka kwace masa mukami tare da tilasta masa mika kadarori guda 18.

Source: Facebook
Tun daga shekarar 1996, ya yi murabus mulki a matsayin Amanyanabo (sarki) na Twon Brass a Jihar Bayelsa.
6. Tsohon gwamnan Oyo ya zama Sarki
Tsohon gwamnan jihar Oyo daga 2003 zuwa 2007, Rasheed Ladoja, ya zama Sarkin Ibadan na 44 a ranar Juma'a, 26 ga Satumba, 2025.

Source: Facebook
Mai Martaba Oba Rashidi Adewolu Ladoja, ya shiga cikin jerin ƴan Najeriya kaɗan da suka samu damar yin mulki a matsayin gwamna sannan daga baya su hau karagar sarauta.
7. Marigayi Sarkin Lere, Abubakar Mohammed
An haifi Abubakar Mohammed a ranar 15 ga Afrilu, 1944 kuma ya halarci makarantar firamare ta Lere da ta Soba tsakanin shekarar 1951 zuwa 1958.
Rahoton Premium Times ya nuna cewa daga baya ya wuce zuwa makarantar Barewa College da ke Zariya daga 1959 zuwa 1963.
Ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello a tsakanin shekarar 1965 zuwa 1966, sannan ya tafi California a Amurka, bayan haka ya shiga rundunar sojin Najeriya.

Source: Twitter
A soja, ya kai matsayin Birgadiya Janar, kuma ya zama gwamnan soja na jihar Sakoto daga watan Agustan 1985 zuwa Satumban 1986.
Marigayi Abubakar Mohammed ya rasu a shekarar 2021 yana da shekaru 76. Ya bar ‘ya’ya hudu da kuma jikoki da dama.
Tinubu ya hallara nada Sarkin Ibadan
A wani rahoton, kun ji cewa manyan 'yan siyasar Najeriya sun dura jihar Oyo ranar Juma'ar da ta wuce nadin sarauta.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cikin wadanda suka hallara nada Sarkin Ibadan na 44.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, sauran Sarakunan gargajiya daga jihohi daban daban ne suka halarci nadin sarautar Oba Ladoja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng




