An Kwantar da Gwamna a Asibiti daga Tafiya Wani Aiki a Kasashen Waje? Gaskiya Ta Fito
- Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya musanta rahoton da ke nuna cewa an kwantar da shi a asibiti a kasar waje
- Nwifuru, wanda bai jima da dawowa Najeriya daga wata ziyarar aiki da ya kai kasashen ketare ba, ya ce yana cikin koshin lafiya
- Ya kuma gargadi masu yada irin wadannan karairayi marasa tushe, inda ya bukaci su shiga taitayinau tun kafin su kai shi bango
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana cewa ya yi mamaki matuka da ganin jita-jitar da ake yadawa cewa yana fama da rashin lafiya.
An dai fara yada labarin cewa an kwantar da Gwamna Nwifuru a gadon asibiti yayin da ya yi wata tafiyar aiki zuwa ƙasashen waje kwanan nan.

Source: Facebook
Daga ina jita-jitar rashin lafiyar ta taso?

Kara karanta wannan
Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci
Vanguard ta ruwaito cewa an yada rade-radin musamman a kafafen sada zumunta cewa gwamnan ya tafi waje ne don neman magani.
Wannan jita-jitar ta jawo damuwa a wasu sassan jihar Ebonyi inda mutane da dama suka fara tada hankulansu kan lafiyar gwamnan.
Sai dai a ranar Laraba yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yanci tare da bikin cikar jihar Ebonyi shekaru 29 da kafuwa, gwamnan ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya sosai.
Da gaske Gwamna Nwifuru ba shi da lafiya?
Gwamna Nwifuru ya karyata jita-jitar, yana mai cewa ya yi wannan tafiya zuwa kasashen ketare cikin koshin lafiya kuma ya dawo lafiya.
Ya ce har mahaifinsa ya kira shi cikin damuwa yana tambayarsa ko lafiyarsa kalau saboda yadda labarin ya yadu kuma mutane suka fara yarda da shi.
Nwifuru ya fayyace cewa babu wata rashin lafiya da ta kama shi a wannan tafiya, yana mai cewa nutsuwa da shiru-shirunsa ke jawo irin wannan jita-jitar mara tushe.
"Mun kyale mutane su yi abin da suke so amma kar ku yi kuskuren kai ni bango. Na yi imanin cewa idan ba ka da muhimmanci, babu wanda zai rika magana a kanka.

Kara karanta wannan
"Mun ceto Naira," Tinubu ya tabo batun darajar kudin Najeriya a jawabin ranar 'yanci
“Wannan ba yana nufin ba za mu iya ɗaukar mataki ba, amma bana so mu fara yin hakan. Idan ka ga mutum mai shiru-shiru, ka yi hankali da shi. Idan na tuna wahalhalun da na sha lafin taka wannan matsayin, sai na hakura kawai.
- Gwamna Nwifuru.

Source: Facebook
Gwamna ya jero nasarorin da ya samu a Ebonyi
Gwamna Francis Nwifuru ya kuma jero nasarorin da gwamnatinsa ta cimma tun bayan hawa kujerar mulki a shekarar 2023, in ji rahoton Punch.
"Ebonyi tana da abin da zai sa ta yi murnar shekaru 29 da kafuwa, kuma ina mika godiya ga tsofaffin gwamnoninmu da shugabannin jihar bisa yadda suka ci gaba da tafiyar da ita cikin haɗin kai tun daga 1996,” in ji shi.
Gwamnan Ebonyi ya dawo da hadimansa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya dawo da jami'an gwamnatinsa 81 bakin aiki bayan dakatarwar da ya masu.
Gwamna Nwifuru ya dakatar da jami'an ne saboda kin halartar wani taron gwamnati, amma dai yanzu ya dawo da su bakin aiki.
Ya umarce su da su dawo bakin aiki nan take ba tare da bata wani lokaci ba domin dorawa daga inda suka tsaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng