An Sace Malamar Asibiti daga Kama Rantsuwar Aiki, 'Yan Bindiga Na Neman N200m

An Sace Malamar Asibiti daga Kama Rantsuwar Aiki, 'Yan Bindiga Na Neman N200m

  • An shiga jimami bayan 'yan bindiga sun yi awon gaba da wata malamar asibiti lokacin da take tafiya a jihar Neja
  • Miyagun sun yi garkuwa da ita lokacin da take kan hanyar komawa gida bayan ta yi rantsuwar kama aiki
  • An yi kira ga hukumomi kan su tabbatar da cewa an kubutar da ita cikin koshin lafiya tare da sada ta da iyalanta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wata malamar asibiti mai suna Basheerah Ojedeyi.

'Yan bindigan sun sace Rad. Basheerah ne lokacin da take kan hanyar komawa gida bayan kammala bikin rantsuwar kama aiki.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da malamar asibiti
Malamar asibiti, Rad. Basheerah Ojedeyi da 'yan bindiga suka sace. Hoto: @Rad_Adebayo, @BashirAhmaad
Source: Twitter

'Yan bindiga sun sace malamar asibiti

A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba 2025, Legit Hausa ta samu labarin wannan mummunan lamari da ya auku.

Kara karanta wannan

DSS sun kwace makaman yan sa kai kafin harin yan bindiga? Gwamnati ta magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shafin @ArewaFactsZone na manhajar X ya sanya labarin cigiyar neman Rad. Basheerah Ojedeyi.

'Yan bindigan sun sace Rad. Basheerah ne a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumban 2025 a kan hanyar komawa gida bayan rantsuwar kama aiki.

Rad. Basheerah Ojedeyi ta kammala karatunta a bangaren Radiography daga jami'ar Usmanu Danfodio (UDUS) da ke jihar Sokoto.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindigan sun sace ta a Neja lokacin da take kan hanyar komawa gida a jihar Osun.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan sun bukaci a ba su N200m a matsayin kudin fansa kafin su bari ta shaki iskar 'yanci.

Kungiyar malaman asibitin ta yi kira ga gwamnati

Kungiyar Association of Radiographers of Nigeria (ARN) ta masu daukar hoto ta nuna takaicinta kan sace malamar asibitin da 'yan bindiga suka yi.

A cikin wata sanarwa da ta aikawa Legit Hausa, kungiyar ta nuna bacin ranta kan sace daya daga cikin 'ya'yanta da tsageru suka yi, bayan murnar bikin rantsuwar kama aiki.

Kara karanta wannan

Saura Turji: 'Yan sanda sun cafke tantirin dan bindiga a Zamfara

Sanarwar na kunshe da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Dr. Musa Y. Dembele.

Kungiyar ta nuna cewa akwai rashin imani wajen neman N200m a matsayin kudin fansa, inda ta bayyana cewa hakan ya jefa rayuwar matashiyar cikin babban hatsari.

An sace malamar asibiti a Neja
Hoton Rad. Basheerah Ojedeyi da 'yan bindiga suka sace. Hoto: @Rad_Adebayo
Source: Twitter

Hakazalika, ta yi kira ga hukumomi da su yi bakin kokarinsu domin ganin an kubutar da ita cikin koshin lafiya.

Ta kuma bayyana cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da cewa an sada Rad. Basheerah tare da iyalanta.

"Kungiyar ARN na kira ga shugaban kasa, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sufeto Janar na 'yan sanda, hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro, kan su yi gaggawar daukar mataki."
"Muna bukatar a dauki kwakkwaran mataki kan rashin tsaron da ke azabtar da 'yan Najeriya, musamman ma'aikatan lafiya wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen ceton wasu."

- Dr. Musa Y. Dembele

Sojoji sun cafke masu taimakon 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar cafke wasu mutane masu hada baki da 'yan bindiga a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane

Dakarun sojojin sun cafke mutanen ne bayan samun bayanai kan ayyukansu a karamar hukumar Kankara.

Mutanen da ake zargin sun amsa cewa suna samar da kayan aiki da suka hada da makamai ga 'yan bindiga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng