"Mun Ceto Naira," Tinubu Ya Tabo Batun Darajar Kudin Najeriya a Jawabin Ranar 'Yanci
- Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa tsare-tsaren gwamnatinsa sun ceto Naira daga kalubalen da ta shiga a kasuwar canji
- Shugaba Tinubu ya ce banbancin da aka rika samu a kasuwannin canji wanada ya kawo cin hanci, ya zama tarihi a yanzu
- Mai Girma Shugaban ya ce farashin canjin Naira da Dalar Amurka ya daina dogaro da farashin danyen mai a kasuwar duniya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ikirarin cewa kudin Najeriya watau Naira ta fita daga kalubale da rashin tabbas da ta shiga a shekarun baya.
Shugaba Tinubu ya ce matakan da gwamnatinsa ta dauka sun ceto Naira daga tangal-tangal da rashin tabbas a shekarun 2023 da 2024.

Source: Facebook
Bola Tinubu ya yi wannan furucin ne a jawabin ranar 'yancin kai da ya yi kai tsaye da yan Najeriya ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya daidaita farashin Naira
Ya jaddada cewa Naira ta samu daidaito a kasuwar hada-hadar kudi ta bayan fage da wacce ke karkashin kulawar gwamnati.
"Tazarar farashin canji a kasuwar gwamnati da kasuwar bayan fage ya ragu matuka sakamakon sauye-sauyen da muka yi da karin zuba jari da shigowar kudin waje."
"Farashin canji mabanbanta da aka rika samu a baya wanda ya haifar da cin hanci da satar dukiyar kasa, yanzu ya zama tarihi.
"Bugu da kari, yanzu farashin canjin Naira da Dalar Amurka ya daina dogaro da farashin danyen mai a kasuwar duniya."
- Shugaba Bola Tinubu.
Halin da Naira ke ciki a kasuwar canji
A watannin baya-bayan nan, darajar Naira ta farfado musamman bayan samun karin kudaden da ’yan kasa ke turo wa daga ketare da kuma rage a gibin farashin canji a kasuwar gwamnati da ta bayan fage.
A wannan ahekarar da muke ciki, mafi munin faduwar darajar Naira shi ne lokacin da aka rika musayar kowace Dalar Amurka a kan N1,637.
A farkon makon nan, Naira ta kara mikewa yayin da Dalar Amurka ke faduwa. A kasuwar musayar kudaden waje ta Najeriya, farashin canji ya dawo ₦1,485.5/$.
Haka kuma, a kasuwar bayan fage, Naira ta dan karfafa a ranar Talata inda ta rufe a ₦1,500/$, sabanin ₦1,510/$ da aka yi musaya makon da ya gabata.

Source: Getty Images
Wane sauyi aka samu a darajar Naira?
Bisa wannan ne, Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa tsare-tsarensa sun farfado da darajar Naira ta hanyar samar da daidaiton farashi a kasuwannim canji.
Ya kuma bai wa yan Najeriya tabbacin cewa farashin canji ya daina dogaro da farashin danyen mai a duniya, cewar rahoton The Cable.
Tinubu ya kara kare kansa kan cire tallafi
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta matakin tsige tallafin man fetur ne domin ceto tattalin arzikin Najeriya.
A jawabinsa na ranar cikar Najeriya shekaru 65 da samun yancin kai, Bola Tinubu ya ve cire tallafin fetur ba abu ne mai sauki ba amma ya zama wajibi.
Shugaban Kasar ya bayyana cewa ya gaji tattalin arzikin da ya kusa durkushewa, don haka dole ne a dauki tsauraran matakai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

