Kwamishinan 'Yan Sanda Ya Fusata Gwamna Abba a Wurin Faretin Ranar 'Yancin Kai a Kano

Kwamishinan 'Yan Sanda Ya Fusata Gwamna Abba a Wurin Faretin Ranar 'Yancin Kai a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa kan abin da kwamishinan yan sandan Kano ya yi a ranar bikin yancin kai
  • Abba ya bayyana halayyar da Kwamishinan ya nuna a matsayin rashin da'a da biyayya, yana mai cewa hakan bai dace ba
  • Gwamnan Kano ya bukaci hukumomin tsaro su guji tsoma kansu a harkokin siyasa domin hakan ba zai amfani kowa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna bacin ransa a fili kan matakin da Kwamishinan ’Yan Sanda jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya dauka a ranar bikin yancin kai.

Gwamna Abba ya zargi CP Ibrahim Bakori da nuna son kai da son zuciya bayan rundunar ’yan sanda ta kauracewa bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da aka gudanar a Kano.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Da yake jawabi a taron da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha yau Laraba, Gwamna Abba ya bayyana kauracewar yan sanda a matsayin cin mutuncin al'ummar Kano, in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya yi kira ga dukkan hukumomin tsaro da su ci gaba da sadaukar da kansu wajen kare martaba da haɗin kan al’ummar wannan ƙasa, ciki har da Kano da sauran jihohi.

Gwamna Abba ya soki Kwamishinan 'Yan Sanda

A rahoton da Premier Radio ya tattaro wani faifan bidiyo, Gwamna Abba ya ce:

"A madadi na a matsayin babban jami'in tsaro a jihar Kano da kuma daukacin jama'ar Kano muna Allah wadai da wannan halayya da kwamishinan 'yan sanda ya nuna."
"Tarihi ba zai manta da shi ba kuma wannan ya nuna rashin kwarewa, son zuciya da rashin kishin kasa, taya za ka jamye jami'an yan sanda daga wannan taro mai cike da tarihi?"

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kaddamar da shirin matasa, kowane zai samu N150,000 a Kano

"Mun yi bakin kokarinmu wajen ganin cewa an samar da tsaro amma abin bakin ciki, kwamishina ya janye jami'an da ke wannan waje, kuma ba da som ransu ba."

- In ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Yadda kwamishinan ya fusata gwamnan Kano

Gwamnan ya nuna bacin rai kan lamarin, yana mai cewa an yi hakan ne da gangan don kunyata jihar Kano da al'ummarta a rana mai tarihi.

“Kamar yadda ku ka gani, a wannan rana ta cikar Najeriya shekaru 65, ya ki zuwa wurin wannan taro tare da dakarunsa, ba mu ji dadin wannan dabi'a ta kwamishinan yan sanda ba gaskiya."
“Yau, kowane ɗan Najeriya na farin cikin ranar yanci, a Kano ma haka ne, domin Kano gari ne mai zaman lafiya kuma mutanen Kano masu son zaman lafiya ne," in ji Abba.

A karshe, Gwamna Abba ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya cire Kwamishinan 'yan sandan Kano nan take saboda wannan halayya ta rashin biyayya da ya nuna.

Kwamishinan Yan Sandan Kano da Gwamna Abba.
Hoton Kwamishinan Yan Sandan Kano, CP Bakori da na Gwamna Abba. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa, Aba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba ya fara tallafawa matasa

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano ya kaddamar da shirin tallafawa matasa da kudin da za su kama sana'a ko bunkasa harkokin kasuwancin su.

Kara karanta wannan

Za a shiga kotu da gwamna bayan kisan 'malami' da ya je yi masa wa'azi har gida

Abba Kabir Yusuf ya ce wannan shiri wani bangare na yunkurin tallafawa matasan jihar Kano domin su dogara da kansu.

Gwamnan ya bayyana cewa matasa maza da mata 5,384 ne za su amfana karkashin wannan shiri wanda shi ne kashi na farko.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262