Rikici Ya Kare: Gwamnati Ta Shawo kan Sabanin Dangote da PENGASSAN
- Gwamnatin tarayya ta yi nasarar shawo kan kungiyar manyan ma'aikatan man fetur na kasa, PENGASSAN kan sabaninta da Matatar Dangote
- A zaman shiga tsakani da aka yi sakanin kamfanin Dangote da kungiyar PENGASSAN an kai ga amincewa da wasu sharudda a bangarorin biyu
- Daga cikinsu, kungiyar PENGASSAN ta hakura, za kuma ta janye yajin aikin da ta tsunduma, wanda ake sa ran zai iya gurgunta kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja– Bayan kwanaki biyu ana zaman sulhu, gwamnatin tarayya ta yi nasarar kawo daidaito tsakanin Matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Dr. Mohammed Maigari Dingyadi, ya fitar da safiyar Laraba.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta bayyana cewa an yi tattaunawa mai tsayi kafin a kai ga warware rikicin da ke kanin Dangote da PENGASSAN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cimma matsaya tsakanin PENGASSAN da Dangote
Business Day ta ruwaito cewa inda aka cimma wasu matakai da suka shafi hakkokin ma’aikata da tsarin aiki.
A cewar Dingyadi
"Shiga kungiya hakki ne na kowanne ma’aikaci bisa tsarin dokokin Najeriya, kuma dole ne a mutunta hakan."
An kuma amince cewa kamfanin Dangote zai fara mayar da ma’aikatan da aka sallama zuwa wasu sassa kamfanin, ba tare da rasa albashinsu ko mukamansu ba.
Haka kuma, ba za a hukunta kowanne ma’aikaci saboda rawar da ya taka a rikicin ba ta hanyar ayyana niyya shiga kungiya.
PENGASSAN za ta janye yajin aiki
Kungiyar PENGASSAN ta bayyana aniyar ta na janye yajin aikin da ta fara, bayan da bangarorin biyu suka cimma matsaya cikin lumana da kwanciyar hankali.

Source: Facebook
Wannan mataki ya biyo bayan taron da aka gudanar a Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA) wanda ya ɗauki lokaci har zuwa safiyar Laraba ana yi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya shiga rikicin Dangote da PENGASSAN, ya fadi abin kunyar da zai faru ga Najeriya
Wannan rikicin ya samo asali ne daga zarge-zargen kungiyar PENGASSAN cewa Matatar Dangote na sallamar ma’aikatan kungiya da maye gurbinsu da ƙasashen waje.
Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani saboda damuwa kan illar da rikicin zai iya yi wa tattalin arzikin ƙasa da kuma bangaren wmakamashi.
A cikin tawagar gwamnati da suka halarci zaman sulhun har da Mallam Nuhu Ribadu; Ministan Kwadago, Dr. Dingyadi; Ministan Kuɗi, Wale Edun.
Sauran sun hada da Ministan Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu; Karamar Ministan Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha; Shugaban DSS, Adeola Ajayi; da Shugaban NIA, Ambasada Mohammed Mohammed.
Gwamna ya magantu kan Dangote da PENGASSAN
A baya, mun ruwaito cewa Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana damuwarsa kan rikicin da ke faruwa tsakanin Kamfanin Dangote da kungiyar ma'aikatan mai ta PENGASSAN.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce idan abubuwa suka kai ga rushewa ko dakile ayyukan matatar, hakan zai zama abin kunya ga Najeriya a idon duniya ganin cewa duka 'yan kasa daya ne.
Ya ce matatar Dangote ba ce ta Dangote kaɗai ba — ta Najeriya ce baki daya, kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
