Bayan Wuya: Tinubu Ya Fadi Yadda Sauki Ya Fara Samu wa a Najeriya

Bayan Wuya: Tinubu Ya Fadi Yadda Sauki Ya Fara Samu wa a Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa lokacin matsananciyar wahala ta kau a Najeriya, za a fara ganin ribar manufofinsa
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga 'yan kasa kan cikar kasar nan shekaru 65 da samun 'yancin kai daga Turawa
  • A cewarsa, Najeriya ta fara fitowa daga cikin mawuyacin halin tattalin arziki da ta tsinci kanta ciki a baya, tare da yi wa jama'a albishir

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja– Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta tsallake siradi madi wahala a kokarin da ake na farfado da tattalin arzikin kasa.

Shugaban da ya kama mulki a shekarar 2023, ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

Shugaba Tinubu ya ce sauki yana samuwa
Hoton Shugaban Kasa, Tinubu na jawabi Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa Bola Tinubu ya bayyana haka ne a yayin jawabin sa na ranar tunawa da cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: Tattalin arziki na farfado wa

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa a cewar Shugaban kasar, gwamnatinsa ta bijiro da wadansu matakai bayan ta tarar da tattalin arzikin Najeriya a gargara.

A cewarsa:

"Gwamnatina na gyara abubuwa cikin gaskiya da rikon amana. Ina farin cikin sanar da ku cewa mun fara samu kanmu, lokacin shan wahala ya shude."
Shugaba Tinubu ya gode wa 'yan Najeriya
Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Tinubu ya yi godiya ga 'yan Najeriya bisa juriya, fahimta da goyon baya, inda ya ce wahalhalun da aka sha a baya na shirin zama tarihi.

Ya ƙara da cewa:

"Zan ci gaba da aiki tukuru don ku da kuma cika alkawuran da na ɗauka na jagorantar Najeriya zuwa sahun gaba."

Tinubu ya fadi ci gaban da Najeriya ta samu

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na samun gagarumar farfaɗowa, inda ya ce GDP ya karu da kaso 4.23 cikin ɗari a zangon biyu na 2025 — mafi girma cikin shekaru hudu.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a yau 1 ga Oktoba 2025

A cewarsa:

"Wannan ci gaba ya zarce hasashen da IMF ta yi na 3.4%. Sauye-sauyen da muka fara shekaru biyu da suka wuce sun fara haifar da gamsassun sakamako."

Ya ce manufofin kuɗi da kasafin kuɗi da gwamnati ke aiwatarwa sun haifar da nasarori guda 12 da suka karfafa tattalin arzikin ƙasa cikin shekaru biyu kacal.

Tinubu ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa 20.12% a watan Agusta 2025 — mafi ƙaranci cikin shekaru uku.

Gwamnatin tarayya na ƙoƙarin bunƙasa aikin noma da rage dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje.

Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun wallafa cewa a yayin bikin shekaru 65 da samun ‘yancin kai na Najeriya, Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi soki gwamnatin Tinubu.

Ya bayyana cewa ko da yake Najeriya na da yalwar albarkatu, mutane da dama sun koma zama ‘yan gudun hijira ko masu neman abinci, saboda rashin kulawa daga gwamnati.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

Atiku ya zargi gwamnatin da sakaci wajen kare rayuka da jin daɗin ’yan Najeriya, inda ya ce yunwa da kashe‑kashe sun addabi sassa daban‑daban amma gwamnati ta zura ido.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng