'Tattali da Tsaro,' Bangarori 23 da Tinubu Ya Tabo a Jawabinsa na Ranar 'Yanci

'Tattali da Tsaro,' Bangarori 23 da Tinubu Ya Tabo a Jawabinsa na Ranar 'Yanci

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya jawabi a ranar Talata, 1 ga Oktoba, yayin bikin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A jawabin nasa, shugaban ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara tun daga 2023 sun riga sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya a ranar samun 'yanci
Shugaba Bola Tinubu na jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai, 2024. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Cikakken jawabin Tinubu na ranar 'yancin kai

Ga cikakken jawabin da Tinubu ya yi, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. ’Yan uwana ’yan Najeriya, yau mun cika shekaru 65 da samun ’yancin kanmu a matsayin babbar ƙasa. Yayin da muke tunawa da wannan rana mai tarihi da nasararmu tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, lokacin da kakanninmu suka karɓi ragamar mulki daga hannun Turawa, ya dace mu tuna da sadaukarwa, kishin kasa da mafarkin kafa ƙasa mai ƙarfi, wadata da haɗin kai wacce za ta jagoranci Afirka kuma ta zama haske ga sauran duniya.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

2. Kakanninmu masu kishin ƙasa—Herbert Macaulay, Dr Nnamdi Azikiwe, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Chief Obafemi Awolowo, Sir Ahmadu Bello, Margaret Ekpo, Anthony Enahoro, Ladoke Akintola, Michael Okpara, Aminu Kano, Funmilayo Ransome-Kuti da sauran jarumai—sun yi imani cewa makomar Najeriya ita ce ta jagoranci bakaken fata gaba ɗaya a matsayin mafi girman ƙasar bakar fara a duniya.
3. Tsawon shekaru, burin samun ’yancin kai ya fuskanci ƙalubale da dama na zamantakewa, tattalin arziki da siyasa, amma mun tsira. Ko da yake ba mu cimma dukkan manyan burukan kakanninmu ba, amma ba mu kauce daga su gaba ɗaya ba. A cikin shekaru 65 da samun ’yanci, mun samu gagarumar nasara a fannin ci gaban tattalin arziki, haɗin kai da kuma cigaban ababen more rayuwa.

Ci gaba a fannin ilimi da kiwon lafiya

4. Duk da cewa wasu suna maida hankali kan abin da ba a iya aiwatarwa ba, amma ya kamata mu yi murnar ci gaban da aka samu. Yanzu ’yan Najeriya suna da damar samun ilimi da kiwon lafiya fiye da yadda aka yi a 1960. A wancan lokaci, muna da makarantun sakandare 120 da ɗalibai 130,000 kacal. Amma a 2024, adadin ya haura zuwa makarantu 23,000. Haka kuma, daga jami’a ɗaya kacal (Ibadan) da Kwalejin Yaba a lokacin samun ’yanci, yanzu muna da jami’o’i 274, kwalejojin fasaha 183 da kwalejojin ilimi 236.

Kara karanta wannan

Bayan wuya: Tinubu ya fadi yadda sauki ya fara samu wa Najeriya

5. A cikin tafiyarmu, mun dandana daɗi da ƙunci. Mun shiga yaƙin basasa, mun rayu ƙarƙashin mulkin soja, mun kuma fuskanci rikice-rikicen siyasa. Amma a kowane lokaci mun yi nasara, mun ci gaba da neman ƙasa ɗaya wacce kowa zai samu damar rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Cigaban mulki da sauyin tattalin arziki

6. ’Yan Najeriya, wannan shi ne karo na uku da zan yi muku jawabi a ranar samun ’yancin kai tun bayan da na hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023. A cikin watanni 28, na jajirce wajen cigaban gina ƙasa kamar kakanninmu da suka gabata.
7. Mun gaji tattalin arziki da ya kusa durƙushewa saboda manufofin da suka rikice. Mun yi zabi: mu ci gaba da yadda aka saba, ko mu kawo sauyi, wanda zai iya sa musha 'yar wahala amma mu ji dadi mai dorewa. Mun zabi hanyar sauyi. A yau, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
8. Mun kawo ƙarshen tallafin mai na bogi da tsarin canjin kuɗi da ya haifar da cin hanci. Mun karkata kudaden zuwa ilimi, lafiya, tsaro, noma da ababen more rayuwa. Yanzu dukkan matakan gwamnati suna da karin kuɗi don kula da talakawa.
9. Muna gina hanyoyi, makarantu da asibitoci da za su kula da al’umma. Mun rasa damar saka hannun jari a da, amma gwamnati a yanzu tana gyara kura-kuran baya.

Kara karanta wannan

Ganduje ya hadu da shugaban kasa, Tinubu ya magantu kan zargin kisan Kiristoci

10. Ina farin cikin sanar da ku cewa mun riga mun tsallake mawuyacin hali. Wahalar jiya tana canzawa zuwa sauƙi. Na gode da hakurin ku.

Nasarorin tattalin arziki

11. A karkashin mulkinmu, tattalin arziki ya fara murmurewa. A karo na biyu na shekarar 2025, GDP ta tashi da 4.23%, mafi girma cikin shekaru hudu. Tashin farashin kaya ya ragu zuwa 20.12%, mafi ƙasa cikin shekaru uku.
12. A cikin shekaru biyu da suka gabata mun samu manyan nasarori guda 12:
– Kudin da ba na mai ba sun karu sosai, mun samu Naira tiriliyan 20 kafin karewar 2025.
– An rage rikon bashi daga 97% zuwa ƙasa da 50%.
– Asusun ajiyar kudin ƙasashen waje ta karu zuwa dala biliyan 42.03.
– Haraji ya tashi daga kasa da 10% zuwa 13.5% na GDP.
– Najeriyar ta zama mai fitar da kayayyaki fiye da shigo da su, tana da ribar cinikayya ta Naira tiriliyan 7.46.
– Samar da danyen mai ya karu zuwa ganga miliyan 1.68 a rana.
– Naira ta daidaita bayan gyaran canjin kuɗi.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a yau 1 ga Oktoba 2025

– An raba Naira biliyan 330 ga gidaje miliyan 8 a shirin tallafin jama’a.
– Noman kwal ya tashi zuwa 57.5% a zango na biyu na shekarar 2025.
– Aikin jiragen ƙasa, hanya da tashoshi suna cigaba.
– An ɗaga matsayin ƙasar wajen darajar kasuwanci a duniya.
– Babban banki ya rage kudin ruwa a karo na farko cikin shekaru 5.
Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta samu ci gaba a fannin tattalin arziki da tsaro a gwamnatinsa
Shugaba Bola Tinubu yana tsaye a zauren majalisar zartawar za a fara taron FEC a Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Nasarorin da aka samu a tsaro

A jawabin shi na bikin 'yancin kai, shugaban na Najeriya ya tabo maganar matsalar tsaro.

13. Rundunonin tsaro suna samun nasara kan ta’addanci, ’yan bindiga da masu satar mutane. An dawo da zaman lafiya a yankunan da aka kwace daga Boko Haram da ’yan ta’adda. Dubban ’yan ƙasa sun koma gidajensu.

Nasarorin da aka samu kan matasa

14. Matasa ku ne makomar ƙasar nan. Ku ci gaba da yin riko da burikanku, kirkire-kirkire da cimma nasarori. Gwamnatina tana tallafa muku ta hanyar manufofi da kuɗaɗe. An kafa NELFUND domin bayar da rancen karatu. Fiye da ɗalibai 510,000 sun amfana.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Bola Tinubu zai yi jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya

15. An bayar da rancen Credicorp na Naira biliyan 30 ga ’yan Najeriya 153,000 don sayen motoci, na’urorin zamani da sauransu.
16. Shirin YouthCred da na yi alkawari a bara yanzu ya zama gaskiya, dubban masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) suna cin gajiyar rancen kayayyaki.
17. An kaddamar da shirin iDICE tare da hadin guiwar AfDB da sauran abokan hulɗa don tallafa wa matasa a fasaha da kirkire-kirkire.

Kalubale da akon fata na-gari

18. Na san cewa gyare-gyarenmu sun zo da dan tsauri, farashin kaya da tsadar rayuwa suna damun jama’a. Amma ba mu da zaɓi na barin tattalin arzikinmu ya ruguje.
19. Nasarar da muka samu ba a lissafin ƙididdiga kaɗai za a auna ba, amma a abincin iyalai, ilimin yara, wutar lantarki a gidaje da tsaron al’umma.
20. Don haka, a wannan cikar shekaru 65, sakona shi ne fata da kira zuwa ga aiki tukuru. Ku rungumi amfani da kayan da aka hada a Najeriya, ku biya haraji, mu gina ƙasa tare.
21. Dole mu yi imani da makomar ƙasar nan, kuma mu yarda za mu yi aiki tare don cimma muradun kasa mai inganci

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Dakarun sojoji sun cafke masu hada baki da 'yan ta'adda a Katsina

22. Da taimakon Allah, sabon babi na rayuwa mai kyau, cike da dogaro da kai na jiran Najeriya nan kusa.
23. Barka da cika shekaru 65 da samun ’yancin kai, Allah ya albarkaci Tarayyar Najeriya. Amin.

Tinubu ya fadi abin da ya gaza yi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya sha ƙoƙarin cimma wani abu a rayuwarsa amma har yanzu bai samu dama ba.

Shugaban kasar Najeriyar ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin rubuta littafi sau da dama, amma haƙar shi bata cimma ruwa ba, dole ya dan tsahirta.

Ya yaba wa Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo bisa rubuta littafi kan nasarorin da jam'iyyar APC ta samu a shekara 10 da suka wuce.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com