DSS Sun Kwace Makaman Yan Sa Kai kafin Harin Yan Bindiga? Gwamnati Ta Magantu

DSS Sun Kwace Makaman Yan Sa Kai kafin Harin Yan Bindiga? Gwamnati Ta Magantu

  • Gwamnatin Kwara ta yi karin haske kan jita-jitar da ake yadawa bayan yan bindiga sun kai mummanan hari a jihar
  • Hukumomi a jihar sun karyata cewa hukumar DSS ta kwace makaman masu gadi a Oke-Ode kafin aka kai hari
  • Harin da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar masu gadi 12 tare da yin garkuwa da wasu mazauna gari da ba su san komai ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara – Gwamnatin Jihar Kwara ta caccaki masu yada rade-radi musamman da ya shafi matsalar tsaro.

Gwamnatin jihar ta karyata zargin da ake yi cewa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kwace makaman masu gadi na sa-kai a Oke-Ode.

Gwamnatin Kwara ta musanta karya da ake yadaw akan tsaro a jihar
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

A cikin wata sanarwa da shafin gwamnatin jihar ta fitar a Facebook, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi jimamin rasa rayuka da aka yi.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun kai mummunan hari a Kwara

An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a Oke-Ode da ke karamar hukumar Ifelodun, kafin mummunan harin da aka kai ranar Lahadi 28 ga watan Satumbar 2025.

Rahoton Legit Hausa ya ce ‘yan bindiga sun afka garin da tsakar dare, inda suka kashe masu gadi 12, suka sace wasu mazauna yankin.

Sannan wasu sun samu raunuka dalilin harin inda aka ce maharan sun fito ne daga dazukan da ke kan iyakar Kwara da Kogi.

Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ta nuna wata mata cikin kuka tana zargin DSS da kwace makaman masu gadin, abin da ta ce ya baiwa maharan damar yin galaba.

Gwamnatin Kwara ta kwantar da hankula

Sai dai kakakin gwamna, Rafiu Ajakaye, ya fitar da sanarwa da Punch ta samu a ranar Talata 30 ga watan Satumbar 2025, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

An lakadawa dan damfara duka bayan asirin shi ya tonu a tsakiyar kasuwar Neja

“Babu gaskiya a zargin cewa DSS ta taba kwace makaman masu gadi. Shugabannin masu gadin daji ma sun karyata wannan magana.”

Ajakaye ya bayyana cewa irin wadannan jita-jita suna batawa jami’an tsaro aiki, yana mai rokon jama’a da su guji yada su.

Gwaman ya fusata game da masu yada karya kan rashin tsaro
Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara. Hoto: Kwara state Government.
Source: Facebook

Gwamna ya karfafawa al'ummarsa guiwa

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kara da cewa wasu kafafen watsa labarai sun yi amfani da hotuna daga wasu wurare don bayar da rahoto, yayin da wasu suka kwatanta lamarin kamar jihar tana cikin yaƙi.

“Za mu fice daga wannan hali cikin kwarin guiwa da tsaro. Mu kasance masu haɗin kai, mu guji yin gaba da kanmu."

- AbdulRahman AbdulRazaq

Rahotanni daga hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa jami’an DSS da sojoji sun halaka wasu daga cikin ‘yan ta’addan a dajin da ke kan iyakar Kwara da Kogi.

Yan bindiga sun kashe dan sanda a Kwara

Mun ba ku labarin cewa mutane sun shiga jimami a jihar Kwara bayan 'yan bindiga sun yi sanadiyyar hallaka wani jami'in dan sanda.

Miyagun sun hallaka dan sandan ne bayan da suka kai hari a wani kamfanin hakar ma'adanai da ke karamar hukumar Patigi.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara ya musanta rahotannin da ke cewa har da jami'ansa aka sace a yayin harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.