Saura Turji: 'Yan Sanda Sun Cafke Tantirin Dan Bindiga a Zamfara
- Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Zamfara na ci gaba da kokari wajen yaki da 'yan bindiga da masu aikata laifuffuka
- Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da jami'an rundunarsa suka samu
- Daga cikin nasarorin har da cafke wani tantirin dan bindiga da ake zargi da laifin yin garkuwa da mutane da dama a jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama sanannen ɗan bindiga, Muhammadu Dan Kani, wanda aka fi sani da “Akki".
Dan bindigan ya fito ne daga kauyen Kuraje a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron manema labarai a hedikwatar rundunar a Gusau a ranar Talata.

Kara karanta wannan
'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka cafke tantirin dan bindiga
CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya ce an kama wanda ake zargin mai shekara 57 a Funtua, jihar Katsina, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna ya yi garkuwa da mutane da dama a fadin jihar.
A cewar kwamishinan, an kama wanda ake zargin da bindigogi 11, harsasai 25 na AK-47 da sauran kayan laifi, rahoton Daily Post ya kawo labarin.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano tushen inda ake samun makaman da kuma cafke sauran mambobin kungiyar ta’addancin.
Hakazalika sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar ya tare wata mota kirar Toyota Corolla yayin aikin sintiri.
Bayan bincike, jami’an sun kwato bindigogin AK-47 guda hudu, harsasai 200 na PKT, harsasai 28 na AK-47 da jigida hudu wadanda babu harsasai a ciki.
An ɓoye makaman ne a cikin buhun lemu mallakar wani mai suna Nasuru Dawan Jiya, wanda ya amsa laifin cewa yana jigilar makaman zuwa wurin ‘yan bindiga a ƙauyen Gurusu.
Kwamishinan 'yan sandan ya ce ana kokarin cafke abokan harkallarsa da kuma rusa gaba ɗaya hanyar samar da makaman.

Source: Twitter
'Yan sanda za su ci gaba da zage damtse
CP Ibrahim Balarabe Maikaba ya jaddada cewa waɗannan nasarorin suna kudirin rundunar ‘yan sandan Zamfara wajen yaki da ta’addanci.
“Ina tabbatarwa mutanen jihar Zamfara cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da jajircewa wajen kawar da ayyukan laifi da tabbatar da tsaron jama'a."
"Muna ci gaba da kira ga jama’a da su riƙa taimakawa ‘yan sanda ta hanyar bayar da bayanai cikin lokaci. Gudunmawarku tana da matukar muhimmanci a wannan yakin".
- CP Ibrahim Balarabe Maikaba
'Yan bindiga sun sace matafiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da matafiya da dama a Neja.
'Yan bindiga sun sace mutanen ne zuwa cikin daji bayan sun tare hanyar da suke tafiya a kanta, a karamar hukumar Mashegu ta jihar.
Daga cikin mutanen da 'yan bindigan suka sace har da kwamishina a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja (NSIEC) da tsohon shugaban hukumar SUBEB.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
