Za a Shiga Kotu da Gwamna bayan Kisan 'Malami' da Ya Je Yi Masa Wa'azi har Gida

Za a Shiga Kotu da Gwamna bayan Kisan 'Malami' da Ya Je Yi Masa Wa'azi har Gida

  • Mahaifiyar matashin Fasto da dan sanda ya harbe har lahira za ta shiga kotu da gwamna domin neman hakkinta
  • Ana zargin an harbe Moses Mba ne yayin da ya je yi wa gwamna wa'azi kan shugabanci da jin tsoron Allah
  • Mahafiyar matashin ta yi alkawarin kai gwamnati kotu bayan danta ya mutu sakamakon harbin jami’an tsaro a Calabar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Calabar, Cross River - Mahaifiyar matashin Fasto, Mrs. Victoria Mba ta gaji da jira inda ya shirya shiga kotu da gwamna.

Ana zargin dan sanda ya harbe matashin, Moses Mba a gaban tsohon gidan Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu.

Za a shiga kotu da gwamna kan kisan Fasto
Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River. Hoto: Governor Bassey Otu.
Source: Twitter

Rahoton Punch ya ce mahaifiyar matashin ta ce za ta kai ƙara, tana zargin gwamnati da yin shiru tsawon wata guda bayan rasuwar ɗanta.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin an kashe Fasto a gidan gwamna

An ruwaito cewa a ranar 1 ga watan Agusta 2025, jami’an tsaro sun harbi Moses, mai shekara 22, suka kuma yi masa duka lokacin da yake ƙoƙarin ganawa da gwamna a Calabar.

Bayan haka, an kai shi Asibitin sojojin ruwa inda aka yi masa tiyata, duk da ƙoƙarin likitoci, ya rasu a ranar 9 ga watan Agusta sakamakon rikicewar ciwon.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce za a yi bincike domin gano hakikanin sanadin mutuwar; ko daga harbin bindiga ne ko kuma daga ciwon da ya biyo baya.

Ana zargin dan sanda da harba Fasto don ya je yiwa gwamna wa'azi
Taswirar jihar Cross River da ke Kudu maso Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Matakin da ake shirin dauka kan kisan

A hirar ta ranar Asabar, mahaifiyar ta bayyana takaicinta kan shiru da alƙawuran karya da ake yi, tana zargin gwamnati da ƙoƙarin rufe maganar da kudi.

Ta ce:

“Mun je wajen su, suka ce gwamna ya tafi. Suka ce zai dawo ranar Asabar. Amma ba a yi komai ba.”

Kara karanta wannan

Kanawa sun fusata, ana zargin 'yan sanda da ajalin wani limami

Victoria ta ce tana shirin shigar da ƙara kotu domin a bayar da diyya da kuma gano masu hannu a ciki.

Ta ƙara da cewa lauyanta a Calabar ya nemi gwamnati ta biya diyya miliyan 100, amma duk da haka babu martani daga gare su.

Mrs. Mba ta ce tana da sunan wanda ya harbi ɗanta kuma za ta fitar da sautin muryar waɗanda suka kawo ta’aziyya a gidanta.

“Abin da nake so yanzu shi ne a yi wa ɗana jana’iza. Dole ne gwamnati ta taimaka wajen kashe kuɗin jana’iza kafin a yi."

- In ji Mbah

Ta ƙara da cewa bayan kusan watanni biyu, gawar ɗanta na nan a dakin ajiyar gawa, ta ce jikinsa ya lalace sosai har ba a gane shi.

A cewarta, gwamnati tana wasa da damuwarta da kuma zafin rashin danta, tana mai cewa za ta ci gaba da neman adalci domin neman hakkin ɗanta.

Gwamna ya tube Sarki kan zargin cin amana

Kun ji cewa Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River ya tsige Ntufam Linus Oben Tabi daga sarautar Mbot Akpa da Ekinta a Akamkpa.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Ana zargin basaraken da karɓar takardar shaida ta bogi da kuma riƙe shugabanci a manyan yankuna biyu lokaci guda.

Gwamnatin jihar ta bayyana matakin a matsayin tabbatar da zaman lafiya da tsari a cikin al’ummomi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.