Katsina: Mutane Sun Yi Kukan Kura, Sun Cafke Ƴan Bindiga da Ke Taimakon Bello Turji
- Hare-haren yan bindiga sun kai mutane bango inda al'ummar wasu yankuna suka fara daukar mataki domin kawo karshen masifar
- Mutanen Ƙadisau a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina sun kama wasu da ake zargin yan bindiga ne
- Daya daga cikin wadanda aka kama ya amsa cewa shi da kansa ya kashe mutane, yana safarar makamai ga Bello Turji
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Faskari, Katsina - Al’ummar Ƙadisau da ke Faskari a Jihar Katsina sun gaji da bala'in hare-haren yan bindiga a yankinsu.
Mutanen garin sun cafke mutane uku da ake zargi da hannu a kai hare-haren ’yan bindiga a yankin.

Source: Facebook
Rahoton Aminiya ya ce mutanen sun miƙa waɗanda suka kama ga jami’an tsaron al’umma domin gudanar da bincike kan wadansa aka cafken.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hare-haren yan bindiga ya kai mutane bango
Jihar Katsina na daga cikin jihohi da suka fi shan fama da hare-haren yan bindiga wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.
Sauran jihohin Arewa da ke shan fama sun hada da Zamfara da Sokoto da Kaduna da kuma Niger a Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
A baya bayan nan, mutane a Sokoto sun dauki doka a hannunsu inda suka yi gaba da gaba da yan ta'adda duba da zargin cewa jami'an tsaro sun gaza kare su daga cin kashi da ake yi musu.
Yadda dan bindiga ke taimakon Bello Turji
Majiyoyi sun tabbatar da cewa tuni jami'an tsaron suka fara yiwa yan bindigar da aka kama tambayoyi domin gano bayanai masu muhimmanci.
Wani daga cikin yan bindiga ya bayyana cewa shi ne ya kashe mutum a harin Ƙadisau saboda an gane shi a lokacin harin.
Ya ƙara da cewa shi mai safarar makamai ne ga ’yan bindigar da Bello Turji ke jagoranta suka kai hari yankin Ƙadisau.

Source: Original
Abin da yan bindigar ke cewa a Katsina
Na biyun ya amsa cewa shi ke safarar abinci, man fetur da kayayyaki zuwa ga wani rikakken dan bindiga mai suna Malam a daji.
Ya kuma bayyana cewa yana cikin wadanda suka kai hare-haren Wasani, Raudama da Unguwar Gizo inda mutane da dama aka kashe tare da sace wasu.
Na ukun kuma ya tabbatar da kai wa Malam kayan abinci, fetur da kayan gona, yana kuma hulɗa da wani jagora mai suna Auwali.
Bisa wannan, hukumomi suka ɗauki waɗannan mutane domin zurfafa bincike kan rawar da suka taka a kashe-kashe, sace-sace da safarar kaya.
Katsina: An kama masu taimakon yan bindiga
A baya, kun ji cewa dubun wasu masu hada baki da 'yan ta'adda ya cika bayan sun fada komar jami'an tsaro a jihar Katsina.
Dakarun sojoji tare da hadin gwiwar jami'an rundunar C-Watch sun samu nasarar cafke mutanen da ake zargi bayan gudanar da bincike.
Hakazalika, sojojin sun kuma samu nasarar ceto wani mutum da 'yan ta'adda suka dauke yana tsaka da aiki a gonarsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


