'Yan Boko Haram Sun Yi Ta'addanci a Borno, An Kona Fadar Basarake, An Kashe Mutane
- 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno, inda suka tafka ta'asa
- Miyagun sun hallaka mutum daya tare da kona gidaje da shaguna na mutanen garin Kirawa da ke karamar hukumar Gwoza
- Sanata Ali Ndume ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya bukaci gwamnati ta kara tura jami'an tsaro zuwa yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Wasu ‘yan ta’addan Boko Haram dauke da makamai sun kai farmaki a garin Kirawa, da ke kan iyaka da Jamhuriyar Kamaru, karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
'Yan ta'addan na Boko Haram sun kashe wani mutum daya sannan suka yi garkuwa da wani namiji a yayin harin.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa 'yan ta’addan sun kona gidaje da dama, ciki har da fadar Hakimin Kirawa, Alhaji Abdulrahman Abubakar, da shaguna da wasu gine-gine.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane sun tsere saboda harin Boko Haram
Yawancin mazauna yankin sun tsere zuwa kauyuka na kasar Kamaru domin tsira da rayukansu, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin mara dadi.
Sun yaba da kokarin ‘yan Civilian JTF da mafarauta waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen dakile harin, lamarin da ya kai ga hallaka ɗaya daga cikin maharan.
A baya, Kirawa na da sansanin sojojin Kamaru, amma an fatattake su a wani hari da aka kai watanni da suka gabata.
Kwana uku kacal da suka gabata, wasu ‘yan ta’adda sun yi kwanton bauna a kan hanyar Kirawa–Pulka, suka kashe ɗaya daga cikin ‘yan sa-kai bayan sun kona motoci guda shida.
Sanata Ndume ya tabbatar da harin
Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata.
"Sababbin hare-haren Boko Haram a Kirawa da sauran yankuna sun zama babban abin damuwa da takaici."
"Musamman ganin cewa yawancin ‘yan gudun hijira masu juriya sun riga sun koma garuruwansu na asali da gwamnatin Gwamna Babagana Zulum ta taimaka wajen dawo da su."
- Sanata Ali Ndume
Yayin da yake yabawa da kokarin sojojin Najeriya wajen yaki da Boko Haram/ISWAP a Arewa maso Gabas, Sanata Ndume, tsohon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojoji, ya yi kira kan a kara tura jami'an tsaro.
Ndume ya bukaci a tura karin sojoji ko manyan rundunoni zuwa yankunan da abin ya shafa kamar Kirawa, Ngoshe, Agapalwa, Chikide da sauran wurare masu fuskantar barazanar hare-hare.

Source: Twitter
Haka kuma ya sake jaddada kira ga gwamnatin tarayya da rundunar sojin Najeriya da su tura jirage marasa matuka, jiragen yaki masu saukar ungulu, kayan aiki da makamai zuwa yankin.
Ya nuna cewa hakan ne kaɗai zai kawo karshen Boko Haram da suka kwashe fiye da shekara 10 a Borno, Arewa maso Gabas da sauran sassan kasar nan.
'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai wani kazamin hari a jihar Borno.
'Yan ta'addan sun kai harin ne a wani sansanin sojoji da ke garin Banki wanda ke kan iyaka a jihar Borno.
Harin ya yi sanadiyyar fatttakar sojoji tare da kwashe makamai masu yawa daga sansanin jami'an tsaron.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


