'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matafiya ciki Har da Kwamishina a Neja
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da fasinjohi masu yawa a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Miyagun 'yan bindiga sun tare hanya ne sannan suka sace fasinjojin bayan sun yi musayar wuta da jami'an 'yan sanda
- Daga cikin mutanen da aka yi awon gaba da su zuwa cikin daji har da tsohon shugaban hukumar SUBEB ta jihar Neja
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zato sun gudo ne daga Kwara, sun sace fasinjoji da dama a Neja.
'Yan bindigan sun sace mutanen ne a kan hanyar Ibbi-Bussa da ke Mokwa–New Bussa a jihar Neja.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta gano cewa cikin waɗanda aka sace har da kwamishina a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Neja (NSIEC), Ahmed Mohammed.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban SUBEB
Hakazalika daga cikin fasinjojin akwai tsohon shugaban hukumar ilmin bai daya ta jihar Neja (NSUBEB), Alhaji Bawa Niworo.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sace fasinjoji da dama daga motocin da 'yan bindigan suka tare a wani daji kusa da Ibbi a karamar hukumar Mashegu ta jihar a daren ranar Litinin.
Majiyoyi sun ce tsohon shugaban SUBEB ɗin tare da wasu mutane ciki har da wani lauya mai suna Barrista Ahmad suna kan hanyarsu ta zuwa Minna ne lokacin da ‘yan ta’addan suka tare hanyar, suka kuma yi awon gaba da su zuwa dajin da ke kusa.
An kuma bayyana cewa sauran mutanen da aka sace ‘yan kasuwa ne da ke dawowa daga kasuwar mako ta New Bussa.
'Yan sandan Neja sun yi bayani
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
"Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a shingen bincike na ‘yan sanda a kan hanyar Ibbi–Bussa. Tawagar ‘yan sanda ta yi musayar wuta tare da korar ‘yan ta’addan."
"A yayin hakan, an lalata motar sintirin ‘yan sanda da harbin bindiga, yayin da ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya samu raunin harbin bindiga, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti don jinya."
"Abin takaici, ‘yan bindigan da suka tsere daga baya sun tare hanya a gaban shingen binciken na ‘yan sanda, inda suka sace wasu fasinjoji daga kusan motoci uku."
- Wasiu Abiodun

Source: Original
Wasiu Abiodun ya ce rundunar ‘yan sanda ta tura karin tawaga tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro da ‘yan sa-kai, domin bin sawun 'yan bindigan da niyyar ceto waɗanda aka sace da kuma cafke miyagun.
Sojoji sun cafke masu hada baki da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin suna hada baki da 'yan bindiga a Katsina.
Sojojin sun cafke mutanen ne guda biyu a karamar hukumar Kankara bayan zarge-zarge sun yi yawa a kansu.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun cafke masu hada baki da 'yan bindiga dauke da kayan laifi a Katsina
Daya daga cikin mutanen da aka cafke ya amsa cewa yana samar da kayan aiki ga 'yan bindigan da ke kai hare-hare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

