Dalilin Nada Sanusi Mikail a Matsayin Sarkin Zuru daga cikin Mutane 40 da Suka Nemi Sarautar
- Sarkin Zuru, Sanusi Mika'il Sami ya jagoranci tawagar masarautar sun kai wa Gwamna Nasir Idirs ziyara a Birnin Kebbi
- Gwamna Nasir ya shaida wa tawagar cewa ya zabi sabon Sarkin Zuru ne saboda shi ne ya fi karbuwa a wurin jama'a
- Mai Martaban ya bayyana cewa sun kawo wa gwamnan ziyara ne domin godiya bisa nadin da ya yi masa da kuma fatan alheri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa ya nada Sanusi Mika'il Sami Gomo na III, a matsayin sabon Sarkin Zuru ne saboda shi jama'a ke so.
Gwamna Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya ce ya nada Sanusi Mika'il ne bayan gano cewa shi ne ya fi shahara da karbuwa a wurin jama'a daga cikin mutane 40 da suka nemi sarautar.

Kara karanta wannan
Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci

Source: Facebook
Sarkin Zuru ya ziyarci gwamnan Kebbi
Gwamnan ya bayyana haka ne a Birnin Kebbi lokacin da sabon Sarkin ya jagoranci babbar tawaga daga masarautar Zuru zuwa gidan gwamnatin Kebbi, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya jagoranci tawagar masarautar zuwa wurin Gwamna Nasir ne domin yi masa godiya bisa abubuwan alherin da ya yi wa yankinsu da kuma nadin da ya yi masa.
Da yake jawabi ga tawagar Sarkin Zuru, Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa bai san Sanusi Mika'il Sami a lokacin da ya nada shi a sarautar ba.
Dalilin nada Sanusi Mikail Sami a sarauta
Ya ce bayan rasuwar Muhammad Sani Sami Gomo II, ya ba da umarnin a binciko wanda jama'a suka fi kauna kuma a ka gabatar masa da Sanusi, take kuma ya nada shi.
“Ni kaina ban san shi ba a da, amma lokacin da kujerar ta zama babu kowa a kanta, na bada umarnin gudanar da bincike sosai kan wanda ya fi karbuwa da amincewar jama’a.
"Ba tare da sabani ba, kowa ya ambaci sunan Sanusi, sai na amince da nadin shi nan take.”
- Gwamna Nasir Idris.
Gwamnan Nasir ya bukaci sabon Sarkin da ya jagoranci jama’arsa cikin adalci, daidaito da gaskiya, jaridar Punch ta ruwaito wannan.

Source: Facebook
Meya sa Sarkin Zuru ya ziyarci gwamnan?
A nasa jawabin, sabon Sarkin ya shaida wa gwamnan cewa ya jagoranci tawaga daga sassan masarautar Zuru domin gode masa bisa karamcin da ya yi masa da al’ummarsa.
Ya ce masarautarsa za ta ci gaba da tuna gwamnan a cikin addu’o’i musamman wajen neman Allah ya ba da nasara a aikin gyaran hanyar Koko-Dabai.
Gwamna Nasir ya dakatar da kwamishina
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Kebbi, Dr Nasir Idris, ya dakatar da kwamishinan lafiya na jihar, Yunusa Isma’il daga mukaminsa saboda zargin da ake yi masa.
Gwamnan ya dauki wannan mataki ne a wurin taron Majalisar Zartarwa ta Kebbi, bisa zargin kwamishinan da sakaci da rashin aiwatar da ayyukan ofishinsa.
Matakin dakatar da kwamishinan na zuwa ne bayan alkawarin da Gwamna Nasir Idris ya dauka na ladabtar da duk jami'in gwamnati da ya yi sakaci da aikinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
