Da Sauran Rina a Kaba: Gwamna Abba Ya Yi Maganar Cikar Najeriya Shekara 65 da 'Yanci

Da Sauran Rina a Kaba: Gwamna Abba Ya Yi Maganar Cikar Najeriya Shekara 65 da 'Yanci

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Najeriya har yanzu ba ta kai matsayin da ya dace da ita ba tun bayan samun 'yancin kai
  • Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da kasar nan ke shirin bikin cika shekaru 65 da samun 'yancin zama kasa mai cikakken iko daga Turawa
  • Ya ce kalubale kamar talauci da rashin tsaro sun hana kasar kai wa mataki da ci gaban da ake so, amma duk da haka, ya ce har yanzu akwai mafita

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa bayan shekaru 65 da samun ‘yancin kai, har yanzu, Najeriya ba ta kai matakin ci gaban da ake bukata ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya aika da muhimmin sako ga jami'an gwamnatinsa

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin wani taron jawabi na musamman kafin bikin ‘yancin kai da aka gudanar a dakin taro na Coronation Hall na Gidan Gwamnatin Kano.

Gwamna Abba ya magantu a kan samun yancin Najeriya
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Gwamnan ya bayyana haka ne ta cikin jawabin da shugaban ma’aikatansa, Dr Sulaiman Wali, ya karanto a madadinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya magantu kan 'yancin Najeriya

Leadership ta ruwaito Gwamnan ya bayyana cewa duk da har yanzu Najeriya ba ta kai ga ci ba, wannan ba ya nufin a yanke kauna da ci gaban kasar nan.

Ya ce:

“Shekaru 65 da samun 'yancin kai, amma har yanzu, akwai doguwar tafiya kafin mu kai inda mu ke fata. Amma wannan ba dalili ba ne na yanke ƙauna; yana nuni ne da bukatar mu tashi tsaye. Haɗin kai ba yana nufin mu zama ɗaya ba ne, sai dai rayu a cikin lumana duk da bambancinmu tare da aiki don makoma ɗaya.”

Ya ƙara da shawartar al’ummar ƙasar nan da su taimaka wajen ina Najeriya ta hanyar shiga harkokin dimokuradiyya a dama da su.

Shawarar Gwamna Abba ga 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Sheikh Triumph: Shugaban Malaman Kano ya kawo mafita kan zargin batanci

Abba Kabir Yusuf ya shawarci jama'a a kan su tallafa wa jagorori wajen shirye-shiryen tsaro da bunƙasa matasa.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa bikin cika shekaru 65 ya kamata ya zama lokaci na tunani da tantance rawar da kowa zai iya takawa wajen samar da haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban kasa.

Gwamna ya ce akwai sauran aiki a Najeriya
Hoton Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A jawabin da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya gabatar, a yayin taron, ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta rayuwar matasa da tsaro.

Ya ce shirin “Safe Corridor Initiative” ya bayar da dama ana shawo kan matsalar ‘yan daba da masu ta’amuli da miyagun ƙwayoyi.

An kama bindigogi a jihar Kano

A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yakin da take da laifuffuka a watan Satumba na shekarar 2025.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.

Kara karanta wannan

'Yar Najeriya da ta shirya kafa tarihin kwanciya da maza 100 a awa 24 ta canza shawara

A cewar CP Bakori, wannan shiri ya taimaka matuka wajen rage laifuffuka da hana su tun kafin su faru, kuma rundunar ta yi nasarar cafke mutane 105 da ake zargi da aikata laifuffuka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng