An Kama Bindigogi AK 47 a Kano, Masu Laifi 105 Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda a Satumba

An Kama Bindigogi AK 47 a Kano, Masu Laifi 105 Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda a Satumba

  • Rundunar ‘yan sanda a Kano ta ce ta samu nasarori wajen dakile laifuffuka a watan Satumba ta hanyar aikin Operation Kukan Kura
  • An kama mutane 105 da ake zargi da laifuffuka, ciki har da fashi da makami, satar mota, safarar miyagun kwayoyi da sauransu
  • An kwato manyan bindigogi, motocin hawa, babura, shanu, na'urorin POS da miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai sama da N82m

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yaki da laifuffuka a watan Satumban 2025, karkashin Operation Kukan Kura.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar a Bompai, Kano.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Dakarun sojoji sun cafke masu hada baki da 'yan ta'adda a Katsina

Wasu daga cikin kayayyakin da 'yan sanda suka kwato a Kano
Wasu daga cikin kayayyakin da 'yan sanda suka kwato a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa rundunar ta kara kaimi wajen dakile laifuffuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa shirin Operation Kukan Kura ya taimaka wajen rage laifuka da hana barazanar tsaro kafin su faru.

An kama bindigogin AK-47 a jihar Kano

A cikin bayanin da ya gabatar, CP Bakori ya ce an samu raguwar laifuffuka tare da kama mutane 105 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka a watan Satumba kadai.

Laifuffukan sun hada da fashi da makami, safarar miyagun kwayoyi, satar motocin hawa, babura da adaidaita sahu, da kuma rikice-rikicen 'yan daba.

Haka kuma, an kwato makamai iri daban-daban ciki har da bindigogin AK-47 guda 3, bindigogin pistol guda 3, bindigu kirar gida 4, alburusai, takubba, wukake da sauran makamai masu hadari.

Baya ga haka, rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa an kwato motocin hawa 7, adaidaita sahu 2, babura 13 da shanu 3.

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: An bayyana sunayen malami da mutum 4 da suka 'mutu' lokaci Guda a masallaci

Wasu daga cikin bindigogin da aka kama a Kano a Satumban 2025.
Wasu daga cikin bindigogin da aka kama a Kano a Satumban 2025. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

An kama miyagun kwayoyi a Kano

Kwamishinan ya ce an kwato kwayoyin Tramadol da Pregabalin da darajarsu ta kai N82,725,000 daga Unguwar Rimin Auzinawa a Kano.

Hakazalika, an kwato tarin tabar wiwi da za a mika ga hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanarwa a gaban kotu.

Wadanda aka kama a Kano da zargin laifuffuka

A cikin wadanda aka kama akwai mutum 17 da ake zargi fashi da makami, takwas da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

An kama mutum tara da ake zargi da satar motocin hawa, biyar da ake zargin satar adaidaita sahu da babura, tara da ake zargi da sace-sace, da 57 da ake zargin shiga fadan daba.

'Yan sanda sun gode wa al’umma

Business Day ta wallafa cewa CP Bakori ya gode wa al’ummar jihar Kano bisa goyon baya da hadin kai da suke bayarwa ga rundunar ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

FBI ta sa ganimar $10, 000 a kan 'dan Najeriya da ake zargi da sata a Bankin Amurka

Ya jaddada cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da amfani da duk wata dabara da ta dace wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano.

Makiyaya sun hana noma a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa manoma sun yi korafi kan wani yanayi maras dadi da suka shiga a karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya taba ziyartar Darazo domin magance matsalar amma hakan bai tsayar da matsalar ba.

Wasu mazauna yankin da suka tattauna da Legit Hausa sun bayyana cewa makiyaya na iya kashe mutum idan suka same shi a gona.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng