Abin da Ya Sa Dole Gwamnonin Arewa Su Yi Magana da Murya Daya kan Matsalar Tsaro
- Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce lokaci ya yi da gwamnonin Arewa za su hada kai wuri guda, su yi magana da murya daya
- Dauda Lawal ya ce babu mai zuba hannun jarin da zai shigo ya zuba dukiyarsa a wurin da babu tsaro a Arewa
- Ya ba da shawarar kulla wata yarjejeniya ko kafa kwamitin da zai rika magana da yawun jihohi 19 na Arewacin kasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bukaci gwamnonin jihohi 19 na Arewa su dunkule wuri daya, su rika magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki.
Gwamna Dauda ya yi wannan kira ne a wurin taron zuba jari da farfado da harkokin masana'antun Arewa da aka gudanar a otal ɗin Abuja Continental.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Dauda Lawal ne ya jagoranci zaman farko na taron, Channels tv ta ruwaito.
Ya bayyana cewa an shirya taron ne ta hannun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi, inda aka haɗa duka manyan masu ruwa da tsaki daga Arewa baki ɗaya.
Gwamna Dauda ya ja hankalin 'yan Arewa
A jawabinsa, Gwamna Lawal ya yaba wa kungiyar saboda jajircewarta wajen ci gaba da fatan ganin Arewa ta magance matsalolin da suka addabe ta.
"Shirya wannan taron kadai ya nuna hangen nesan wannan kungiya duba da take da aka ba shi na, 'bude damarmakin da mu ke da su', kuma an zabi fannoni masu muhimmanci, ma'adanai, noma da lantarki.
"A Zamfara, mun san irin matsalar da muke fuskanta: ƙasa mai yalwar ma’adanai da filayen noma masu faɗi, amma mutanenmu ba su amfana da albarkatun ba.”
“Tambayar da ke gabanmu a matsayin shugabanni ba wai me za a yi ba ne, amma ta yaya za mu haɗa kai mu sauya damar da muke da ita zuwa arziki? Dole mu ajiye komai, mu hada kanmu.
- Gwamna Dauda Lawal.
Abin da ya kamata gwamnonin Arewa su yi
Gwamna Lawal ya nanata cewa tsaro a Arewa shi ne kashin bayan zuba jari, yana mai jan hankalin gwamnonim jihohin Arewa 19 da su fifita hada kai fiye da siyasa.
A rahoton Daily Trust, Gwamna Dauda ya kara da cewa:
“Dole mu haɗa kai wajen tsare rayukan mutane da jawo masu zuba hannun jari. Tsaro shi ne tubalin farko na kowane ci gaba."
“Shawara ta ita ce ne mu kafa Northern Nigerian Economic Compact, wato wata yarjejeniya ta haɗin kai tsakanin jihohi 19 na Arewa domin yin magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki."

Source: Facebook
Gwamna Dauda ya ce babu maganar sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal ya sake nanata matsayarsa kan sulhu da 'yan ta'addar da ke kashe mutanen Zamfara ba dare ba rana.
Gwamna Dauda Lawal ya fadawa mutanen Zamfara cewa gwamnatinsa na nan a kan bakarta cewa ba za ta taba yin sulhu da 'yan bindiga ba.

Kara karanta wannan
Gwamna ya gwangwaje magidanta da tallafi bayan tsuntsaye da kwari sun tafka barna
Gwamnan ya ce a lokacin da yake shiga kauyukan, ya fahimci titunansu sun lalace don haka ya yi alkawarin gyara masu domin su ma su samu saukin zirga-zirga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

