Tajudeen: Shugaba Majalisa Ya Hango Lokacin Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Najeriya

Tajudeen: Shugaba Majalisa Ya Hango Lokacin Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Najeriya

  • Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya kan batun rashin tsaro
  • Tajudeen Abbas ya bayyana cewa nan da wani dan lokaci za a daina batun matsalar rashin tsaro a Najeriya
  • Shugaban majalisar ya kuma yi magana kan shirin da shugaban Bola Tinubu yake yi don kawo karshen matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas PhD, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.

Tajudeen Abbas ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kudiri aniyar kawar da matsalar tsaro a Najeriya.

Tajudeen Abbas ya yi magana kan rashin tsaro
Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas Hoto: @Speaker_Abbas
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta ce shugaban majalisar wakilan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ranar Lahadi a wani taron da ofishin shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa ya shirya a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasar nan ta fuskanci ƙaruwa a hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane don neman kudin fansa, da kuma dawowar ayyukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi sun tanka bayan ADC ta ba'yan hadaka umarni

Me Tajudeen ya ce kan rashin tsaro?

Tajudeen Abbas ya ce gwamnatin Tinubu za ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya ba su sake shiga damuwa kan batun tsaro ba.

"Babu wata kasa a duniya da za ta iya samun ci gaba mai ma’ana ba tare da tsaro ba."

- Tajudeen Abbas

Ya bayyana cewa shugaban kasa da majalisar dokoki sun yi aiki tukuru wajen samar da hanyoyin magance matsalar tsaro ba tare da amfani da karfin soja kaɗai ba, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar da labarin.

“Misali a jihata ta Kaduna, a makonni biyu da suka gabata jakadan Birtaniya a Najeriya ya bai wa Gwamna Uba Sani lambar yabo saboda ci gaba ta fuskar tsaro da aka samu a jihar."
"Ina da yakinin cewa cikin shekara biyu masu zuwa, kuma tabbas cikin shekara huɗu na wannan gwamnati ba za mu sake tattaunawa kan matsalar tsaro ba."
"Saboda gwamnati za ta ɗauki duk matakan da suka wajaba don samar da yanayin da zai rage barazana da kuma kawo karshen matsalar gaba ɗaya.”

Kara karanta wannan

ADC ko ADA: 'Yan hadaka sun kammala zabar jam'iyyar da za su yi takara a 2027

- Tajudeen Abbas

Najeriya za ta samu karin kudi

Tajudeen Abbas ya ce Najeriya za ta samu karuwar kudi a kasafin kuɗinta na shekara-shekara, musamman ta hanyar gyaran tsarin haraji da ake sa ran zai inganta samun kuɗaɗen shiga.

Tajudeen Abbas ya ba da tabbaci kan matsalar rashin tsaro
Tajudeen Abbas a wajen wani taro Hoto: @Speaker_Abbas
Source: Twitter
“Idan aka kalli adadin kuɗin da aka warewa sassa kamar ilimi da lafiya a kasafin kuɗi na baya-bayan nan, za a ga akwai karin kuɗi idan aka kwatanta da shekarun baya."
"Babban kalubalenmu shi ne karancin kuɗin shiga. Amma shugaban kasa da majalisa sun kawo sabuwar dabara da za ta kara yawan kuɗaɗen shiga na Najeriya cikin shekara ɗaya zuwa biyu masu zuwa."

- Tajudeen Abbas

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Kwara.

'Yan bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Ifelodun, inda suka hallaka jam'an tsaro na 'yan sa-kai da mafarauta.

Kara karanta wannan

"Za ku iya rasa kimarku": Tinubu ya aika da gagarumin saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya

Mummunan harin ya yi sanadiyyar rasuwar jami'an tsaro 15 bayan 'yan bindigan sun farmake su a inda suke yin aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng