'Yan Bindiga Sun Shiga har Gida Sun Datsa Sarkin Fulani da Adda a Neja

'Yan Bindiga Sun Shiga har Gida Sun Datsa Sarkin Fulani da Adda a Neja

  • Wasu ‘yan bindiga sun kashe Sarkin Fulanin Tungan-Madugu, Abu Bani-Gene, a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja
  • Rahotanni sun ce an ce maharan sun kai farmaki gidansa da safiyar Lahadi inda suka yi masa sara da adda har ya mutu
  • Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da sakin fasinjojin da aka sace a hanyar Kontagora–Zuru bayan bincike mai zurfi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja – Wasu mutane dauke da makamai sun kashe Sarkin Fulanin Tungan-Madugu da ke yankin Babanna a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Wannan hari ya auku ne da safiyar Lahadi a gidansa, inda aka ce sun sassara shi da adda har ya riga mu gidan gaskiya.

Taswirar jihar Neja da aka kashe Sarkin Fulani a cikinta
Taswirar jihar Neja da aka kashe Sarkin Fulani a cikinta. Hoto: Legit
Source: Original

Legit ta tattaro bayanai kan kisan gillan da aka yi wa Sarkin Fulanin ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda 'Dan sanda ya harbe kansa har lahira a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa tuni aka kai gawarsa asibitin Babanna domin yin binciken likitoci kafin a yi masa jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.

An kashe Sarkin Fulani a Neja

Wanda aka kashe shi ne Abu Bani-Gene mai shekaru 65, wanda ya kasance Sarkin Fulani a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa maharan ba su yi amfani da bindiga ba sai adda, abin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tsananin fargaba.

Mazauna yankin sun bayyana cewa tuni ake shirin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Matakan jami’an tsaro bayan kisan

Hukumomi sun tabbatar da cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin domin gano wadanda suka aikata wannan ta’asa.

Sun ce rundunonin tsaro sun bazama a yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma kama wadanda suka aikata kisan.

Al’ummar yankin sun nemi gwamnati ta dauki matakai masu tsauri don dakile irin wadannan hare-hare da ke addabar su ba dare ba rana.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari, an rasa rayukan jami'an tsaro a Kwara

Gwamnan jihar Neja, Umaru Muhammad Bago
Gwamnan jihar Neja, Umaru Muhammad Bago. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

An sake wadanda aka sace a Neja

A wani bangare na daban, rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da sakin fasinjoji da aka sace a hanyar Kontagora–Zuru.

An bayyana cewa wata mota kirar Toyota Corolla ce da ta dauki fasinjojin ta gamu da ‘yan bindiga a kauyen Gulbin-Boka a ranar Asabar da yamma.

Sai dai rundunar ta ce bayan tsauraran matakan da jami’an tsaro suka dauka, an samu nasarar ganin fasinjojin sun kubuta ba tare da an cutar da su ba.

Rundunar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da bincike domin kama wadanda suka yi garkuwa da fasinjojin.

Makiyaya sun hana noma a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa mutanen karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi sun koka da cewa wasu makiyaya sun hana su zuwa gona cikin kwanciyar hankali.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen yankin sun ce makiyayan za su iya kashe mutum, su kona masa abin hawa idan suka same shi yana aiki a gona.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya ziyarci karamar hukumar domin kawo karshen rikicin amma mazauna yankin sun ce babu abin da ya canja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng