Sheikh Triumph: Shugaban Malaman Kano Ya Kawo Mafita kan Zargin Batanci

Sheikh Triumph: Shugaban Malaman Kano Ya Kawo Mafita kan Zargin Batanci

  • Sheikh Ibrahim Khalil ya ce ba za a iya warware rikicin malamai da ake fama da shi a Kano hanyar mukabala da juna ba
  • Malamin ya bukaci a koma kan tsarin Shehu Usman Dan Fodiyo wajen warware matsalolin addini da suke faruwa a Kano
  • Baya ga haka, Shehin ya gargadi malamai da mabiyan Izala da Darika da su tsaya a layinsu ba tare da zargin juna da batanci ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi tsokaci kan korafe-korafen da aka shigar kan maganganun Sheikh Lawal Abubakar Triumph.

Malamin ya bayyana cewa babu tabbacin cewa za a shawo kan rikicin malamai a Kano ta hanyar mukabala watau yin zama domin a baje hujjoji.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda 'Dan sanda ya harbe kansa har lahira a Kano

Shugaban malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil
Shugaban malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil. Hoto: Khalil Network
Source: Facebook

A bidiyon da Radiyon Premier ya wallafa a Facebook, Malamin ya ce kowa na ikirarin shi ne kan gaskiya, kowa na cewa yana kare addini, lamarin da ya ce ba zai kawo karshen rigimar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mafitar da Sheikh Ibrahim Khalil ya kawo

Sheikh Khalil ya bayyana cewa hanyar samun mafita ita ce a nemo tushen matsalolin domin a warware su, maimakon yin mukabala.

Ya nuna cewa idan ‘yan Darika suka tsaya kan harkokinsu, haka ma wadanda ba 'yan Darika ba suka guji tsoma baki wajen karantar da littattafan Darika, hakan zai iya kawo sauki.

A Kano, k wanan nan an ji malaman da ba su cikin darika suna karantar da littatafai irinsu Jawahirul Ma'ani.

Ya ce tarihi ya nuna cewa Shehu Usman Dan Fodiyo ya yi wa’azi da ya shafi kowa cikin natsuwa, ba tare da tada rikici ko batanci da ya iya haifar da rabuwar kai ba.

Kara karanta wannan

Zargin taba annabi: Sheikh Bala Lau ya magantu kan rawar hukumar DSS a Kano

A kan maganar kai kara wajen kwamitin shura, Sheikh Khalil ya ce kusan kowane malami yana da wakilai a kwamitin kuma za su iya goyon bayansa.

Bukatar bin tsarin Usman Dan Fodiyo

Sheikh Ibrahim Khalil ya yi kira da a koma kan tsarin da Shehu Usman Dan Fodiyo ya bari domin kawo sauki a cikin harkokin addini.

A cewarsa, bin tsari da fahimtar juna ne kaɗai zai iya kawo karshen fitina da ake fama da ita tsakanin mabiya kungiyoyi.

Sheikh Triumph da aka shigar da korafi game da shi
Sheikh Triumph da aka shigar da korafi game da shi. Hoto: Sheikh Abubakar Lawal Shuaibu Triumph
Source: Facebook

Ya bayyana cewa ya dace malamai na Izala su tsaya a cikin tsarin da suka dauka, haka ma ‘yan Darika su tsaya a nasu tsarin, ba tare da kawo abubuwan da za su haifar da rikici ba.

Malamin ya yi gargadin cewa abin da ake yi yanzu, na zargin juna da cewa wani makiyin Annabi ko wani ya saba addini, ba zai kawo ci gaba ba, illa tayar da hankali a cikin al’umma.

Gargadi ga malamai da mabiyansu

Sheikh Khalil ya yi nuni da cewa ya kamata malamai da mabiya su guji amfani da batanci da misalai marasa kyau wajen bata juna.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Ya kuma tuna cewa a da, irin su Imam Shafi’i, suna gudanar da tattaunawa da mukabala da sauran malamai ne domin neman fahimtar juna, ba domin bata ko neman suna ba.

Ana son kafa doka kan batanci a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wasu malamai a jihar Kano sun zauna da sakataren gwamnatin jihar kan zargin da aka yi wa Sheikh Lawal Triumph.

Yayin tattaunawar da suka yi, Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya yi magana kan yadda za a shawo kan zargin mutane da batanci.

Sheikh Gadon kaya ya ce ya kamata gwamnatin Kano ta kafa dokar hana jama'a gama gari ikirarin cewa wani ya yi batanci a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng