Babu Magudi: Jonathan, Osinbajo da Jega na Wani Shirin Kawo Sauyi a Zaben 2027
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo za su bukaci gyara a zaben Najeriya
- Taron zai gudana a Abuja ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, a daidai lokacin da Najeriya ke bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai
- Ana sa ran tattaunawar za ta fitar da muhimmiyar takarda kunshe da bukatu da za a mikawa manyan hukumomi da jam’iyyun siyasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Yayin da kasar ke bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, jiga-jigan siyasa da shugabanni a Najeriya za su taru domin taron kasa kan gyaran tsarin zabe.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne zai shugabanci zaman, inda tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, zai kasance a matsayin mataimaki.

Source: Facebook
Leadership ta wallafa cewa taron na da nufin tattaunawa da amincewa kan manyan matakan da za su taimaka wajen tabbatar da sahihin zabe a shekarar 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin da za su halarci taron
Baya ga Jonathan da Osinbajo, tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega, tsohuwar ministar ilimi, Dokta Oby Ezekwesili za su hallara.
Haka zalika an bayyana cewa sanannen lauya Dr Olisa Agbakoba, da kuma masanin siyasar tattalin arziki Farfesa Pat Utomi za su je taron.
Wadannan shugabanni za su hada kai da NCFront, LCSF, NERCO, da sauran kungiyoyi wajen gudanar da taron.
Taron zai gudana ne a babban birnin tarayya Abuja karkashin taken “muhimman gyaran kundin tsarin mulki don sahihin zabe a 2027.”
Me za a tattauna a taron zaben?
Manufar taron ita ce samar da matsaya kan batutuwa da dama, ciki har da tabbatar da tura sakamakon zabe ta yanar gizo.
Za a tattauna kan yadda ‘yan kasa za su rika taka rawa wajen nada shugabannin INEC, samar da cikakken ‘yanci ga INEC wajen samar da kudin hukumar zabe.
Haka zalika za a tattauna matakan da ya kamata a bi wajen lura da kuma kulawa da kudin jam’iyyun siyasa.
Ana son tattauna matsalolin jam'iyyu na cikin gida, amfani da fasahar zamani a zabe, da kuma karfafawa matasa, mata da masu bukata ta musamman shiga harkokin siyasa.
Dalilin yunkurin gyaran zaben 2027
Masu shirya taron sun bayyana cewa zaben 2023 ya tona wasu manyan matsaloli da ke cikin tsarin zaben Najeriya.
Sun ce wajibi ne a dauki matakai cikin gaggawa domin kauce wa matsalolin da ka iya rage sahihancin zaben gaba.
Saboda haka, za a mayar da hankali kan kawar da sayen kuri’u, hana tashin hankali a lokacin zabe, da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a.

Source: Facebook
Daga karshe, za a fitar da takarda mai kunshe da bukatun gyaran zabe, wadda za a mika wa majalisar dokoki ta kasa, hukumar INEC, jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Ana sa ran wannan yunkuri zai taimaka wajen gina tsarin zabe mai inganci da karfafa dimokuradiyya a Najeriya.
Matakan nada shugaban INEC
A wani rahoton, kun ji cewa an fara maganar nada sabon shugaban hukumar INEC bayan wa'adin Farfesa Mahmud Yakubu ya kusa karewa.
Kallo ya koma kan shugaba Bola Ahmed Tinubu domin duba wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu.
A kan haka ne Legit Hausa ta hada rahoto na musamman a kan matakan da a ke bi wajen nada shugaban INEC a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


