Talauci da Rashin Tsaro Sun Tilasta wa Manyan Arewa Zama a Abuja don Nemo Mafita
- Wasu daga cikin manyan Arewa sun fara zama a Abuja domin nemo hanyar warware matsalolin da su ka addabi shiyyar na tsaro da talauci
- Mai magana da yawun ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jiddare ya bayyana cewa taron zai zama dandali haska albarkatun ma’adanai da ke yankin
- An gayyaci gwamnonin jihohi 14 na Arewa da na Abuja domin su halarci taron tare da masu zuba jari da kokarin farfado da yankin baki dayansa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Dattawan Arewa a karkashin NEF ta fara gudanar da wani taron kwanaki biyu a babban birnin tarayya Abuja.
Kungiyar na taron ne domin tattauna hanyoyin farfaɗo da tattalin arziƙin yankin Arewa da kuma fitar da al’umma daga kangin talauci.

Source: Twitter
BBC Hausa ta wallafa cewa Mai magana da yawun ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jiddare, ya shaida cewa taron na da nufin haskaka irin albarkatu da damammakin da ke yankin Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan Arewa suna taron tattalin arziki
Farfesa Abubakar Jiddare ya ce babban burin taron shi ne jawo hankalin masu zuba jari, domin su ga irin abubuwan da Arewa ke da su.
Ya kara cewa:
“Mun tsara taron ne ta yadda idan ka zo, za ka san inda ma’adanai su ke, a wace jiha su ke, da yadda za a iya zuba jari, da kafa masana’antu da kuma sarrafa su."
Ya kara da cewa yankin Arewa na fama da yawan matasa marasa aikin yi, kuma abin ya ke kara dagula rayuwar jama’a da haifar da rashin zaman lafiya a wasu sassan.
Saboda haka, ya ce lokaci ya yi da za a farka daga dogaro da gwamnatin tarayya, a fuskanci cigaba ta hanyar amfani da albarkatun yankin.
Dattawan Arewa na neman sauki a Najeriya
Farfesa Jiddare ya ce sun gayyaci gwamnonin jihohi 14 na yankin da kuma na babban birnin tarayya, Abuja, domin su halarci wannan muhimmin taro.
Taron, wanda aka fara a yau, zai bai wa mahalarta damar yin musayar ra’ayi tare da ganin irin abubuwan da ke akwai a Arewa, musamman ma’adanai da za a iya amfani da su wajen kafa masana’antu.

Source: Twitter
Ya ce:
“Kowa ya sani yadda tattalin arziƙin Arewa ya koma baya, Muna son mu fitar da yankin daga cikin wannan mawuyacin hali.”
Ƙungiyar ta ce wannan taro wani mataki ne na mayar da hankali kan abin da Arewa ke da shi, ba wai abin da take nema daga wasu ba.
NEF na fatan wannan taron zai zamo wata kafa ta shawo kan matsalolin yankin ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.
Tsaro: Dattawan Arewa sun cimma matsaya
A wani labarin, kun ji cewa a labarin nan, za a ji cewa dattawan Area sun bayyana takaici, inda su ka shaida wa Shugaban Kasa na cikin wani mawuyacin hali na rashin tsaro.
Ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dauki matakin gaggawa ta hanyar ayyana dokar ta-baci domin dakile barnar da ‘yan bindiga ke yi da kuma samun damar magance matsalar.
Wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere, ya sanya hannu, NEF ta ce lamarin garkuwa da jama'a da kashe mutane ba dare ba rana ya wuce gona da iri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


