Shiga Sharo ba Shanu: Yan Ta’addan Lakurawa Sun Hallaka Mata kan Zargin Maita
- Hankulan mutane a wani yankin jihar Sokoto sun tashi bayan samun gawar wata mata da ake zargin an hallaka ta
- Ana zargin yan ta'addan Lakurawa sun kashe wata mata mai suna Mai-Kudi Danginjo kan zargin maita da ake yi mata
- Lamarin ya faru ne a garin Tummunna, Gidan-Madi da ke jihar Sokoto bayan zargin a safiyar ranar Asabar 27 ga watan Satumbar 2025
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sokoto - Mutane sun shiga tashin hankali bayan tsintar gawar wata mata a ranar Asabar 27 ga watan Satumbar 2025 a jihar Sokoto.
Majiyoyi sun tabbatar da samun gawar matar da aka kiyasta shekarunta ya kai 45 a kauyen Tummunna, Gidan-Madi a jihar.

Source: Twitter
Rahoton Zagazola Makama ya ce ana zargin yan ta'addan Lakurawa ne suka hallaka matar tare da yar da gawarta a yankin.
Yadda Lakurawa ke addabar al'ummar Sokoto
Lakurawa sun yi kaurin suna a jihar Sokoto wanda a baya suka sheke ayarsu tare da yin barazana ga yan bindiga kan su bi su ko su bar yankin.
Majiyoyi da ke kusa da gwamnati sun bayyana yadda yan ta'addan ke kara yawa inda ya tabbatar da cewa farko ba su wuce mutane 50 ba.
Har yanzu, Lakurawa na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna musamman a jihohin Sokoto da Kebbi da ke makwabtaka da juna.
Wani hadimin shugaban karamar hukumar Tangaza, Gazal Aliyu ya taba bayyana yadda Lakurawa ke sauya limamai a wasu yankunan jihar.
Ya ce:
"Abin takaici yanzu Lakurawa suna zuwa kauyuka suna kwace bindigogi a hannun yan sa kai na 'Community Guard'.
"Suna zuwa gari su gwada ilimin liman, idan bai ci ba, su ba shi kashi, su sauya shi da wani."

Kara karanta wannan
Abin ya yi muni: An bayyana sunayen malami da mutum 4 da suka 'mutu' lokaci Guda a masallaci

Source: Original
Lakurawa sun hallaka mata kan zargin maita
An tabbatar da cewa an kashe matar mai suna Mai-Kudi Danginjo, mai shekaru 45, a ƙauyen Tummunna bayan Lakurawan sun zarge ta da maita.
Lamarin ya faru ranar Asabar, lokacin da ‘yan bindiga da dama suka afka cikin ƙauyen, suka yi awon gaba da ita.
Wasu majiyoyi sun ce da safiyar Lahadi 28 ga watan Satumbar 2025, waɗanda da ake zargin sun dawo cikin ƙauyen suka ajiye gawar matar.
An turo sojojo yankin da abin ya faru
Bayan haka, dakarun Operation FANSAN YANMA sun isa yankin domin gudanar da bincike tare da tashi tsaye wajen neman waɗanda suka aikata laifin.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa ƙoƙarin kamawa da hukunta waɗanda ke da hannu a wannan mummunan lamari yana gudana a halin yanzu.
Lakurawa sun hallaka basarake a Sokoto
Kun ji cewa 'yan ta'addan Lakura dauke da miyagun makamai sun kai hari wani kauyen jihar Sokoto, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.
Wata majiya ta shaida cewa 'yan ta'addar sun kashe hakimin ƙauyen Sayinna da yayan wani mazaunin ƙauyen a wannan farmaki.
Wani rahoto ya nuna cewa mutane sun tsere daga gidajensu yayin da shugabannin gargajiya ke yin hijira saboda hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

