Zargin Kisan Kiristoci: An ‘Gano’ Wadanda Aka Fi Hallakawa a Najeriya
- Reno Omokri ya yi magana kan zargin wani mai gabatar da shirye-shirye na Amurka da ya ce ana kashe Kiristoci a Najeriya
- Ya bayyana cewa babu wata hujjar adadin da aka ambata, inda ya nuna rahoton Global Terrorism Index ya ce mutum 8,352 ne suka mutu bara
- Omokri ya ƙara da cewa hare-haren ’yan ta’adda sun rutsa da Musulmai fiye da Kiristoci, ya zargi masu ƙoƙarin tayar da rikicin addini
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsohon mai taimakawa shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya fusata bayan rade-radin cewa ana yawan kashe Kiristoci a Najeriya.
Omokri ya karyata ikirarin da wani mai gabatar da shirye-shiryen siyasa na Amurka, Bill Maher, ya yi cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya.

Source: Facebook
Omokri ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Omokri ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafin X a jiya Lahadi 28 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki.
Tsohon hadimin shugaban kasa ya ce bidiyon da aka yada na wani mutum kamar dan Najeriya ya yi ikirarin cewa an kashe fiye da Kiristoci dubu 500,000, ba gaskiya ba ne.
Ya ce rahoton 'Global Terrorism Index' na shekarar 2024 ya nuna cewa mutane 8,352 ne suka mutu daga hare-haren ta’addanci da rashin tsaro a bara.
Omokri ya ce ba za a iya cewa Kiristoci 500,000 aka kashe a Najeriya ba, kamar yadda Maher ko wasu rahotanni na ƙarya suka nuna.
Ya kuma bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya ta shafi rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya, ta’addancin Boko Haram da ƙungiyoyin ’yan bindiga.
Ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu tana ɗaukar matakai na kamawa, gurfanarwa da kuma kawar da yan ta’adda da kuma shugabannin manyan ƙungiyoyin ’yan bindiga a Arewa.

Source: Facebook
Omokri ya fadi wadanda aka fi kashewa
Omokri ya ƙara da cewa an kashe sama da manyan ’yan bindiga 16 da suka addabi mutane a Arewa, ciki har da Kachalla Ali Kawaje da sauransu.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda na yi wa Kiristocin Najeriya kisan kiyashi? Minista ya tsage gaskiya
Ya nuna cewa rikice-rikicen sun rutsa da Musulmai da Kiristoci, inda Musulmai suka fi yawa a cikin waɗanda suka mutu daga hare-haren.
Ya jaddada cewa rahoton ACLED ya bayyana cewa daga 2010 zuwa 2023, mutane 13,485 suka mutu a Arewa maso Yamma, mafi yawansu Musulmai.
Ya kammala da cewa ikirarin da aka yi kan kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne, kuma farfaganda ce daga masu neman tayar da husuma a tsakanin al’umma.
Rashin mutunta Sarki: Omokri ya dura kan Obi
A baya, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya fuskanci suka bayan taya sabon Sarkin Ibadan murnar hawa sarauta.
Peter Obi ya kira sabon Olubadan, Oba Rashidi Ladoja, “dabuwa”, abin da Reno Omokri ya kira rashin da'a da girmama basaraken.
Omokri ya ce matsayinsa na Olubadan ya wuce haka, ya gargadi Obi da ka da ya yi abin da ba zai yi wa Sarki ba a Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
