Dadi Ya Kare: Gwamna Ya Sallami Kwamishina bayan Sauye Sauyen Mukamai a Bauchi
- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwa wanda ya raba wata kwamishina da kujerarta
- Gwamna Bala ya cire Hajiya Zainab Baban-Takko daga mukaminta na Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Yara
- Hadimin gwamnan a bangaren harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya bayyana dalilin cire ta daga mukamin da ta ke kai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bauchi - Gwamatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta yi sauye-sauye a majalisar zartarwar jihar.
Gwamna Bala ya sallami Hajiya Zainab Baban-Takko daga mukaminta na Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Yara cikin gaggawa.

Source: Facebook
Gwamna ya kori kwamishina a Bauchi
Sanarwar tsige ta ta fito ne daga Mukhtar Gidado, mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai, a jiya Lahadi, 28 ga Satumba, 2025 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
Bayan yin garambawul, Gwamna Abba ya mika sunaye ga majalisa don nada kwamishinoni
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gidado ya ce tsige kwamishinar na daga cikin sauye-sauyen da gwamna ya yi a cikin tsarin majalisar zartarwar jihar Bauchi.
Sanarwar ta ce:
“A wannan dalili, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Yara, Hajiya Zainab Baban-Takko, ta sauka daga mukaminta da gaggawa.”
Gwamnan ya gode mata bisa gudummawar da ta bayar ga jihar, inda ya yi mata fatan nasara a duk abin da ta sanya a gaba.
Hakan ya zo kwanaki bayan wasu sauye-sauye a majalisar, ciki har da tsige wasu manyan jami’ai, da kuma nadin sababbin mukarraban gwamnati.
A baya-bayan nan, gwamnan ya yi sauye-sauye a mukaman tsaro da sauran muhimman ma’aikatu, don daidaita tsarin mulkin jihar cikin tsari.
Wannan sabon sauyi ya sake nuna cewa gwamnan yana ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don ƙarfafa tafiyar gwamnati da gudanarwa.

Source: Facebook
Abin da kwamishinar da aka sallama ta ce
Har ila yau, kwamishinar da aka sallama ta yi magana bayan rasa kujerar inda ta yi wa Allah godiya da kuma Gwamna Bala Mohammed.
Hajiya Zainab ta bayyana haka ne da safiyar yau Litinin 29 ga watan Satumbar 2025 a cikin wani dogon rubutu a shafinta na Facebook.
Ta ce ta karbi wannan hukunci daga mai girma gwamna cikin tawakkali da yarda da kaddarar Allah kuma cikin kwanciyar hankali.
Hajiya Zainab ta ƙara gode wa Mai Girma Gwamna bisa amincewar da ya nuna a kanta a lokuta daban-daban, tun a matsayin Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu.
Daga baya kuma ya aminta da ita a matsayin Ciyaman ɗin Riko na Ƙaramar Hukumar Bauchi, sannan kuma a matsayin Kwamishina na Harkokin Mata da Ci gaban Yara.
Daga karshe ta yi addu'ar Allah ya albarkaci jihar Bauchi kuma ya saka da alheri ga duk wani ƙoƙari da ake yi don hidimar ɗan Adam.
Bauchi: Gwamna Bala ya sallami jami'an gwamnati
A wani labarin, gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Bala Mohammed ta gano wasu manyan jami'ai biyu da ke amfani da takardun bogi.
Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnati a Bauchi ta kori jami'an daga aiki a wani bangare na tsaftace harkokin aikin gwamnati.
Bayan haka, hukumar ta kara wa wasu ma'aikata girma ciki har da daraktoci da mataimakansu, da wasu lauyoyin gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

