Sardaunan Zazzau: Za a yi Gagarumin Bikin Nadin Sarautar Namadi Sambo a Zariya
- An shirya naɗin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, a matsayin Sardaunan Zazzau a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025
- Bukukuwan naɗin za su gudana a fadar Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, tare da halartar manyan baki daga sassa daban-daban
- An karrama Namadi Sambo ne bisa gudunmawarsa ga ci gaban ƙasa da kuma dangantakarsa da Zazzau, wanda nan ne mahaifarsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Majalisar masarautar Zazzau ta sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin naɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, Sardaunan Zazzau.
Wannan naɗin zai gudana a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025, a fadar mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli.

Source: Twitter
Tun a shekarar 2023 ne masarautar Zazzau ta wallafa a X cewa an ba tsohon mataimakin shugaban kasar matsayin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu mukaman da Namadi Sambo ya rike
Namadi Sambo ya rike mukamin mataimakin shugaban ƙasa daga 2010 zuwa 2015 karkashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.
Kafin haka, ya yi gwamna a jihar Kaduna daga 2007 zuwa 2010, wanda hakan ya ƙara karfafa zumuncinsa da yankin da aka haife shi.
Matsayin Sardauna na ɗaya daga cikin manyan mukamai a masarautar, wanda ake ba mutanen da suka nuna jajircewa da jagoranci wajen ciyar da al’umma gaba.

Source: Facebook
Namadi Sambo ya zama Sardaunan Zazzau
A cewar sanarwar da majalisar masarautar ta fitar, an naɗa Namadi Sambo a matsayin Sardaunan Zazzau tun a shekarar 2023.
Rahoton jaridar Leadership ta wallafa cewa a yanzu ne za a gudanar da bukukuwan naɗin a bainar jama’a.
Naɗin zai sanya shi zama na biyu a tarihin rike mukamin, bayan marigayi Muhammadu Jummare, wanda shi ne na farko da Sarkin Zazzau, marigayi Shehu Idris ya bai wa irin matsayin.
A cewar majalisar, wannan matsayin na daga cikin na fi daraja a masarautar, wanda ke ɗauke da tarihi na ɗaukaka da girmamawa ga wanda ya samu.
Shirye-shiryen biki da bakin da ake jira
A bikin naɗin da za a gudanar a fadar sarki a Zaria, ana sa ran zai jawo manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasa.
Kasancewar shi tsohon gwaman kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, ana sa ran 'yan siyasa, sarakunan gargajiya, jakadu da kuma ‘yan kasuwa za su halarci nadin.
Gudunmawar Namadi Sambo ga ƙasa
Masarautar ta ce ɗaukaka Namadi Sambo zuwa matsayin Sardaunan Zazzau ya samo asali ne daga gudunmawar da ya bayar ga ci gaban ƙasa da masarautar.
Ta ce, a matsayinsa na tsohon gwamna da kuma mataimakin shugaban ƙasa, ya taka rawar gani wajen aiwatar da ayyuka a fannoni daban-daban.
An nada sabon Sarki a Ibadan
A wani rahoton, kun ji cewa an gudanar da bikin nadin sabon Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja a jihar Oyo.
Oba Rashidi Ladoja da ya kasance tsohon gwamnan jihar Oyo ne, ya samu damar zama Sarkin Ibadan na 44.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Rabiu Kwankwaso da wasu manyan mutane ne suka hallara Oyo ranar Juma'ar da ta wuce.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


