Gwamnatin Tinubu Ta Kira PENGASSAN da Dangote, Za a Hau Teburin Sulhu

Gwamnatin Tinubu Ta Kira PENGASSAN da Dangote, Za a Hau Teburin Sulhu

  • Gwamnatin tarayya ta kira shugabannin ƙungiyar ma’aikatan PENGASSAN da kuma shugabannin matatar man Dangote
  • Ta yi kiran domin bangarorin biyu su halarci taron gaggawa domin warware rikici da ya ɓarke tsakaninsu don kaucewa matsaloli
  • Ministan Kwadago da aikin yi, Maigari Dingyadi ne ya kira bangarorin biyu bayan PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan Kwadago, Maigari Dingyadi, ya bayyana takaicin yakin aikin da kungiyar ma'aikatan man fetur a kungiyar PENGASSAN dinka tsunduma.

Ya yi gargadi cewa yajin aikin zai kawo cikas ga tsaron ƙasa da tattalin arziki, sannan ya roƙi ɓangarorin biyu su bai wa gwamnati damar sasanta su.

Gwamnati ta ce akwai matsala idan PENGASSAN ta shiga yajin aiki
Hoton Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da matatar mai Hoto: Getty
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin tsakanin PENGASSAN da matatar Dangote ya kai kololuwa a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tayin da matatar Dangote ta yi wa PENGASSAN kan ma'aikatan da ta kora

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikici ya ƙara zafi tsakanin PENGASSAN da Dangote

Jaridar The Nation ta wallafa cewa PENGASSAN ta umarci 'ya'yanta a faɗin ƙasa su dakatar da ayyukansu.

Wannan umarni ya biyo bayan korar akalla ma’aikata 800 da ke cikin ƙungiyar a cikin matatar Dangote a karshen makon da ya wuce.

Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwarta cewa irin wannan rikici zai haifar da matsaloli ga tattalin arzikin ƙasar da harkokin tsaro.

Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Maigari Dingyadi, ya ce:

“Wannan rikicin ba zai tsaya ga ɓangarorin biyu kawai ba, zai shafi duka al’umma da tattalin arzikin ƙasa. Don haka ina roƙon shugabannin PENGASSAN da su janye yajin aiki su ba mu dama mu yi sulhu cikin yanayi na lumana.”

Gwamnati ta mika takarda ga PENGASSAN, Dangote

Rahotanni sun ce Ma’aikatar Kwadago ta aika takardar gayyata ga shugabannin PENGASSAN da matatar Dangote.

A cikin takardar, an gayyaci bangarorin biyu su halarci aron sasanci a ofishin Minista da ke babban birnin tarayya, Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yadda sakon WhatsApp ya jawo matatar Dangote ta kori ma'aikata 800

Gwamnatin Tinubu za ta taka wa yajin aiki burki
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hi Oyo: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kakakin ma’aikatar, Patience Onuobia, ta jaddada maganar minista inda ta ce:

"Ina roƙon dukkannin ɓangarorin da su tuna muhimmancin fannin man fetur ga ƙasar nan, domin shi ne ginshiƙin tattalin arzikinta."
"Yajin aiki ba zai haifar da koma-baya ga kuɗaɗen shiga kawai ba, zai kuma ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali. Idan aka ci gaba da wannan rikici, zai jawo matsala tattalin arziki.”

Ta ce gwamnati tana da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen tabbatar da adalci, sannan ta yi kira ga ɓangarorin biyu da su yi haƙuri da juna.

Fetur bai fara tsada ba

Abubakar Rabi'u Dangoro, guda ne daga cikin matasa da ke da babur a jihar Kano. Ya shaida wa Legit cewa duk da tataburza tsakanin PENGASSAN da Dangote , ba a samu karin farashin fetur ba.

Ya ce:

"Na sayi lita N830, amma akwai masu sayar wa a kan N870 zuwa N900."

Kara karanta wannan

Rikici ya kare: Gwamnati ta shawo kan sabanin Dangote da PENGASSAN

Kungiyar PENGASSAN ta rufe matatar Dangote

A wani labarin, mun wallafa cewa kungiyar ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta Najeriya, PENGASSAN, ta umarci 'ya'yanta da su janye ayyukansu a faɗin ƙasar.

Wannan mataki ya biyo bayan sallamar ma’aikata fiye da 800 daga matatar Dangote da ke Legas, lamarin da PENGASSAN ta ce ba za ta zuba ido a kai na.

A cikin sanarwar da babban sakataren kungiya, Lumumba Okugbawa, ya fitar, ana cewa an kori ma’aikatan ne saboda shiga ƙungiyar domin kare hakkokinsu,

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng