Kanawa Sun Fusata, Ana Zargin 'Yan Sanda da Ajalin Wani Limami

Kanawa Sun Fusata, Ana Zargin 'Yan Sanda da Ajalin Wani Limami

  • Al’ummar Kuntau a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano sun shiga cikin alhini bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman
  • Ana zargin matashin mai shekaru 24 da ke jan sallah a unguwarsu ya rasu ne a ofishin 'yan sanda bayan sun zo har gida sun yi awon gaba da shi
  • Mahaifinsa, Sheikh Adam Usman, ya ce na’urar CCTV ta nuna jami’an ‘yan sanda biyu suna dukan ɗansa lokacin da su ka zo kama shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoJama'a sun fada a cikin alhini da fushi bayan rasuwar wani limami mai shekaru 24, Salim Usman, inda ake zargin 'yan sanda ne su ka yi ajalinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 22 ga watan Satumba, ‘yan sanda sun kama Salim daga gidansa da ke unguwar Kuntau jim kaɗan bayan ya jagoranci sallar Magariba.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda 'Dan sanda ya harbe kansa har lahira a Kano

Ana zargin 'yan sanda da azabtar da limami a Kano
Hoton Kakakin rundunar yan sandan Kano, SP Kiyawa Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an ce an kama shi ne bisa zargin sayen buhun fulawa da aka sace a bara kamar yadda wani da ake bincike ya shaida masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Matashi ya rasu a komar 'yan sanda

The Cable ta ruwaito cewa Sheikh Adam Usman, mahaifin marigayin, ya shaida cewa na’urar CCTV ta nuna jami’an ‘yan sanda biyu suna cin zarafin ɗansa a lokacin kama shi.

Ya ƙara da cewa an ci gaba da yi masa duka a lokacin da ake tsare da shi, wanda a cewarsa hakan ne ya haifar da mutuwarsa a ranar da aka kama shi.

Sheikh Usman ya bayyana cewa sun kai ƙorafi a hukumance ga rundunar ‘yan sanda, inda aka sanar da su cewa an kama wasu jami’an da ake zargi da rashin bin ƙa’ida wajen aikinsu.

An yi jana'izar limami a Kano
Hoton wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Ya ce:

“An gaya mana cewa an kama wasu jami’an da suka aikata cin zarafi, kuma bincike na gudana a kan lamarin."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari, an rasa rayukan jami'an tsaro a Kwara

An birne matashin limami a Kano

Bayan kwanaki hudu da kama shi, an saki gawar Salim a ranar 26 ga Satumba domin iyalansa su yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya yi umarni.

Wannan na zuwa ne bayan an kammala gudanar da binciken likitanci a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da kotu ta amince da shi.

Ana sa ran rahoton binciken zai fito cikin makonni huɗu masu zuwa domin yin karin haske a kan musabbabin mutuwar Salim a hannun 'yan sanda.

Rundunar 'yan sandan ta bakin Kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ba ta komai a kan faruwar al'amarin ba har kawo wanan lokaci.

'Dan sanda ya harbe kansa a Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa wani jami’in ƴan sanda mai mukamin Sufeto, Aminu Ibrahim, ya rasu a yayin da bindigarsa ta harbe shi bisa kuskure yana bakin aiki.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, yayin da marigayin ke bakin aiki a wani kamfani da aka tura shi domin tabbatar da tsaro ga kamfanin.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan bindiga ke koro mutane a Sakkwato, an tilasta wa jama'a hijira

Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa Aminu Ibrahim ya shiga bandaki tare da bindigarsa, amma yayin da yake zaune, bindigar ta harbi shi bisa kuskure har ya rasu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng