Tirƙashi: PENGASSAN Ta Rufe Matatar Ɗangote, Za a Samu Ƙarancin Fetur a Najeriya

Tirƙashi: PENGASSAN Ta Rufe Matatar Ɗangote, Za a Samu Ƙarancin Fetur a Najeriya

  • PENGASSAN ta rufe matatar man Dangote da ke Legas bayan sallamar ma’aikata kimanin 800 a Najeriya
  • Kungiyar ta ce an sallami ma’aikatan ne saboda shiga PENGASSAN sannan aka maye gurbinsu da baki
  • Rikicin ya samo asali daga sabanin NUPENG da matatar kan ‘yancin kafa kungiya da hakkokin ma’aikata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas- Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur ta Najeriya, PENGASSAN, ta umarci mambobinta a duk fadin kasar nan da su janye ayyukansu.

PENGASSAN ta shiga yakin aiki a faɗin ƙasar ne sakamakon sallamar ma’aikata fiye da 800 da matatar Dangote ta yi.

Ma'aikatan fetur sun rufe matatar Dangote da ke Legas
Hoton Alhaji Aliko Dangote, shugaban kamfanonin Dangote, da ma'aikacin gidan fetur. Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Rikicin ma’aikata da matatar man Dangote

Umarnin shiga yajin aikin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar, Lumumba Okugbawa, ya fitar, in ji rahoton AIT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, kungiyar ta bayyana korar ma'aikata a matatar Dangote a matsayin karya hakkokin kwadago da kuma abin da ka iya zama barazana ga sauran kamfanoni.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kira PENGASSAN da Dangote, za a hau teburin sulhu

Tun da fari, Dangote ya ce ba sallamar ma'aikatan aka haka kurum ba, ya yi haka ne don sake fasalin bangaren ma'aikata, saboda zargin “zagon ƙasa” a wasu sassa na matatar.

Alakar da ta taba kasancewa mai kyau tsakanin ma’aikatan bangaren mai da iskar gas da kuma matatar Dangote yanzu ta rikide zuwa rikici.

Wannan na zuwa ne bayan cece-kuce kan yadda aka hana ma’aikata kafa kungiyarsu ta kwadago a matatar.

Kungiyar PENGASSAN ta shiga yajin aiki a ƙasa

PENGASSAN ta umarci mambobinta a dukkan kamfanonin mai da hukumomi su fara yajin aiki daga daren Lahadi, abin da ka iya haddasa karin karancin mai a kasa.

Yajin aikin ya hada da rufe dakin kula da ayyuka, da kuma rage isar da danyen mai da gas zuwa matatar Dangote.

Kungiyar ta yi zargin cewa ma’aikatan Najeriya ne aka sallama saboda sun shiga PENGASSAN, sannan aka maye gurbinsu da wasu ma'aikatan daga kasashen waje, abin da ta kira “bauta” ga ‘yan kasar.

Matsayin PENGASSAN da martanin Dangote

Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, ya tabbatar da cewa yanzu da suka shiga yajin aiki, komai ya tsaya cak a matatar man Dangote.

Kara karanta wannan

PENGASSAN: 'Abu 1 da Dangote zai yi don hana ƙarancin fetur a Najeriya'

Festus Osifo ya kuma ce an dakatar da aiki a bangaren taki (Train 2), yayin da Train 1 ke aiki da 60%, sai dai bangaren dizal yana ci gaba da aiki.

A gefe guda, har yanzu shugabancin matatar Dangote bai fitar da wata sanarwa ba kan matakin kungiyar.

A baya dai, Dangote ya ce matakin garambawul da yake dauka na da nufin kawo karshen zagon kasa da kuma tabbatar da dorewar ayyukan matatar.

Kungiyar PENGASSAN ta ce ta tsunduma yajin aiki saboa Dangote ya kori ma'aikata 800
Shugaban kungiyar PENGASSAN yana jawabi a wani taro kan makamashi a Abuja. Hoto: @pengassan
Source: Twitter

Rikicin ya samo asali daga NUPENG

Tun farko dai rikicin ya samo asali ne daga kungiyoyin NUPENG da PENGASSAN kan yadda matatar Dangote ke gudanar da harkokin ma’aikata.

NUPENG ta taba zargin cewa an hana sababbin direbobin tankar shiga kungiyar PTD, sannan aka kafa wata kungiyar cikin gida domin kula da jin dadin ma’aikata, abin da ta ce ya saba dokokin kwadago na Najeriya.

Daga baya, an yi taruka tsakanin gwamnati, DSS, NUPENG da Dangote, inda aka dakatar da wani yajin aiki.

Sai dai abubuwa suka sake rikicewa lokacin da matatar ta fitar da wata sanarwa ta bukatar ma’aikata su fice daga PENGASSAN, abin da ya tayar da wannan sabon rikici.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: Ana yi wa Dangote barazana kan matatarsa bayan korar ma'aikata

Dangote ya daina hulda da wasu ƴan kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta dakatar da sayar da kaya ga wasu ’yan kasuwa tun daga 18 ga Satumbar 2025.

Matatar Dangote ta fayyace cewa matakin ya biyo bayan gyara ne don inganta aiki tare da tilasta ’yan kasuwa shiga tsarin 'rarraba fetur kyauta'

Dangote ya kuma nemi afuwar duk wani cikas da hakan ka iya jawowa, yana mai cewa tsarin zai daidaita samar da kaya da rage farashi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com