Tsautsayi: Yadda 'Dan Sanda Ya Harbe Kansa har Lahira a Kano

Tsautsayi: Yadda 'Dan Sanda Ya Harbe Kansa har Lahira a Kano

  • Wani 'dan sanda mai suna Aminu Ibrahim ya yi ajalin kansa bisa kuskure a yayin da ya ke bakin aiki a unguwar Hotoro da ke jihar Kano
  • Rahotanni sun bayyana cewa jama'a sun ji karar harbi, lamarin da ya tada masu hankali su ka ruga domin ganin abin da ya faru da kai dauki
  • Sai dai da isarsu wurin da Aminu Ibrahim ya ke, sai su ka tarar da shi ya harbi cikinsa, kuma alamu na nuna cewa tun a lokacin ya rasu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani jami’in ƴan sanda mai mukamin Sufeto, mai suna Aminu Ibrahim, ya gamu da ajalinsa ta hannunsa bisa kukure.

'Dan sandan ya rasa ransa bayan da bindigarsa ta harbe shi ciki a yayin da yake bakin aiki a unguwar Hotoro,da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kanawa sun fusata, ana zargin 'yan sanda da ajalin wani limami

'Dan sanda ya harbe kashe kansa a Kano
Hoton Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori da wasu jami'an 'yan sanda Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar yayin da marigayin yake aiki a wani kamfani da aka tura shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan sanda ya kashe kansa bisa kuskure

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa wata majiya daga rundunar ƴan sandan Kano ta ce Ibrahim ya je bandaki, amma yayin da yake zaune bindigarsa ta yi harbi ta bugi cikinsa.

Rahoton ya kara da cewa nan take Aminu ya ce ga garinku nan ba tun kafin a yi yunkurin nema masa kulawar likitoci.

Majiyar ta ce:

“Ya tafi bandaki da bindiga, yayin da yake zaune harbin ya tashi ya shiga cikinsa, nan take ya faɗi ƙasa ya mutu."

Ma’aikatan kamfanin sun ce sun ji karar harbi ne, sai suka yi maza suka nufi wurin suka iske jami’in yana kwance rai ya riga ya yi halinsa.

Yadda bindiga ta kufcewa 'Dan sanda

Kara karanta wannan

'Yar Najeriya da ta shirya kafa tarihin kwanciya da maza 100 a awa 24 ta canza shawara

Rahoton ya ci gaba da cewa a ranar Lahadi cewa an gano bindigan da Aminu Ibrahim ke ɗauke da ita mai lamba GT 4177.

Ya bayyana cewa an samu tabbacin bindigan ba ta cikin tanayi rashin tsaro, kuma ya harba harsashi guda ɗaya da ta yi ajalinsa, yayin da harsashi 29 suka rage daga cikin 30 da aka bashi.

An garzaya da Aminu Ibrahim zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda likitan da ke aiki a lokacin ya tabbatar da mutuwarsa.

Ana zurfafa bincike a kan mutuwar 'Dan sanda a Kano
Hoton Kakakin rundunar yan sandan Kano, SP Kiyawa Hoto: Haruna Abdullahi Kiyawa
Source: Facebook

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida cewa ba zai iya fitar da cikakken bayani yanzu ba.

Amma kwamishinan ƴan sanda zai yi taron manema labarai a ranar Litinin domin fayyace batun da sauran abubuwan da suka faru a jihar.

Yan sandan Kano sun fara bincike

A baya, mun wallafa cewa Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da fara bincike kan wani jami’in ‘yan sanda tare da wasu mutane biyu da ake zargin suna karya dokar aiki.

Wani bawan Allah ne ya fara korafi a kan jami'an, inda ya ce suna taimaka wa ƴan daba da karɓar cin hanci daga barayin da ake zargi da aikata laifuffuka a unguwar Sheka a Kano.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan ramin hakar ma'adanai ya rufta da sama da mutane 100 a Zamfara

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar lamarin kafin a dauki mataki na gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng