Zargin Taba Annabi: Sheikh Bala Lau Ya Magantu kan Rawar Hukumar DSS a Kano

Zargin Taba Annabi: Sheikh Bala Lau Ya Magantu kan Rawar Hukumar DSS a Kano

  • Shugaban Izala reshen Kaduna, Sheikh Bala Lau, ya yi magana kan abin da ke faruwa game da Sheikh Shu'aibu Lawan Triumph
  • Bala Lau ya yaba da rawar da shugaban DSS, Mr. Oluwatosin Ajayi, ya taka wajen sasanta rikicin Kano cikin ruwan sanyi
  • Malamin ya bayyana haka a Ibadan, inda ya ja hankalin mabiya su ci gaba da tallafa wa zaman lafiya da haɗin kan Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Shugaban kungiyar Izalah, Sheikh Bala Lau, shugaban Izala na ƙasa, ya yaba da shugaban DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi.

Sheikh Bala Lau ya kwarara yabon ne ga Adeola bisa rawar da ya taka wajen sasanta rikicin addini da ke shirin tashi a Kano.

Bala Lau ya yabawa DSS kan dakile rigima a Kano
Shugaban Izalah, Abdullahi Bala Lau da shugaban DSS, Ouwatosin Adeola Ajayi. Hoto: Abdullahi Bala Lau.
Source: Facebook

Lawan Triumph: Bala Lau ya yabawa DSS a Kano

Ya bayyana haka ne yayin wa’azi a Ibadan, inda ya ja hankalin mabiya da su ci gaba da tallafa wa zaman lafiya da haɗin kai, cewar rahoton Zagazola Makama.

Kara karanta wannan

Komai na iya faruwa: Shugaban APC ya sanya labule da Farfesa Pantami a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala Lau ya tuna cewa rikicin ya bulla a Kano kan shari’ar Malam Abubakar Lawal, wato Triumph, amma DSS ta taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan lamarin.

A cewarsa, an fara shirin gurfanar da Lawal Triumph gaban kotu, sai dai DSS ta umurci hukumar a Kano ta shiga tsakanin mazahabobin Musulunci.

Sheikh Bala Lau ya ce wannan mataki na nuna basira da gaggawar daukar mataki da shugaban DSS ya yi, domin ya tsayar da rikicin cikin lumana.

Ya kuma yi kira ga majalisar Shura a Kano, wadda gwamnati ta nada, da ta tabbatar da adalci da gaskiya wajen bincike domin zaman lafiya.

Bala Lau ya yi magana kan abin da ke faruwa da Lawan Triumph
Shugaban kungiyar Izalah, Sheikh Abdullahi Bala Lau. Hoto: Abdullahi Bala Lau.
Source: Facebook

Addu'o'in da Bala Lau ya yi ga shugabanni

Sheikh Bala Lau ya yi addu’a ga shugabanni da al’umma, yana rokon Allah ya ja-goranci kowa wajen kawo cigaba da zaman lafiya a ƙasa.

Ya kuma shawarci mambobin Izala da su kasance jakadu nagari na addini, ta hanyar yada saƙon Musulunci da hikima da kuma juriya.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya hade 'yan Izala da Darika, ya masu nasiha mai ratsa zuciya kan Tinubu

Ya ce:

“Shekaru da dama ina godiya da goyon bayan Ahlus-Sunnah a Ibadan. Ina kira ku yada kyakkyawan saƙon Musulunci da juriya ga sauran addinai.”

Abin da ake zargin Triumph a Kano

Hakan ya biyo bayan rigimar da ke neman tashi game da kalaman Sheikh Lawan Triumph da wasu ke ganin cin mutunci ne ga Annabi SAW.

Lamarin ya fara daukar wani salo gwamnatin Kano ta dauki mataki da kuma mika korafin da ake yi ga kwamitin Shura a jihar domin samo mafita kan lamarin.

An mika lamarin Triumoh ga kwamitin Shura

A baya, kun ji cewa Kwamitin Shura na jihar Kano ya fara zama kan korafe-korafen da jama'a suka shigar kan Sheikh Lawal Abubakar Triumph.

Wannan zama na zuwa ne bayan gwamnatin Kano ta hannun sakatarenta ta mika duk korafe-korafen ga kwamitin don yin abin da ya dace.

Kwamitin ya bayyana cewa zai gayyaci masu korafi da Sheikh Triumph domin bai wa kowane bangare damar gabatar da hujjoji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com