Wahala da Kara Tunkaro 'Yan Najeriya Sakamakon Matakin da Matatar Dangote Ta Dauka
- Matakin da matatar Dangote ta dauka cewa za ta daina sayarwa yan kasuwa fetur da Naira na iya jawo tsadar kowace lita a gidan mai
- Kungiyar Yan Kasuwar Fetur ta Najeriya (IPMAN) ce ta bayyana haka, inda ta ce matukar matakin ya tabbata to fetur zai tashi
- Man fetur dai na cikin muhimmna abubuwan da yan Najeriya ke amfani da su, wanda ke jawo tsadar sufuri da farashin kayan abinci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta bayyana cewa dakatar da sayar da man fetur a Naira da Matatar Dangote ta yi, zai kara tsadar feturin a kasa.
Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Shettima, ya ce matakin Matatar Dangote zai kara tashin farashin fetur a gidajen mai saboda yanayin matsalar canjin kudi.

Source: Getty Images
Ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Premium Times a safiyar yau Asabar, 27 ga watan Satumba, 2025.
Abubakar Shettima ya tabbatar da cewa wannan mataki ba zai kawo ƙarancin fetur ba, ganin cewa akwai matatar da ke tace mai a ƙasar nan.
Matakin Matatar Dangote zai kara tsadar fetur
Sai dai ya jaddada cewa idan matatar Dangote ta fara sayar da man fetur da Dalar Amurka, tabbas farashin zai tashi.
“Eh gaskiya ne, kamar yadda kuka gani, mu ma haka muka ga labarin kuma tabbas zai shafi farashin fetur.
"Idan matatar ta koma kasuwanci da Daloli, to za a samu kari a farashin kowace litar fetur,” in ji Shettima.
Kungiyar IPMAN ha kira taron NEC
Ya ƙara da cewa ya shirya kiran taron mambobin kwamitin zartarwa (NEC) na IPMAN a ranar Litinin domin tattauna batun da kuma illolin da ka iya biyo baya.
“Bayan sun turo mana sakon wannan mataki ta sakon imel, take na kira mambobin NEC ta nemi zu zo ranar Litinin mu zauna mu tattauna.
"Daga nan kuma mu je mu gana da shugabancin Matatar Dangote domin mu tattauna, mu ga illolin da za su biyo baya.”
Za a shiga karancin man fetur a Najeriya?
Da aka tambaye shi ko wannan mataki zai shafi samar da man fetur, Shettima ya ce:
“A’a, ba zai shafi samarwa ba, tunda muna da matatarda ke tace mai a ƙasar nan, za a ci gaba da samun isasshen man fetur.”

Source: Getty Images
Matatar Dangote, a wata sanarwa da ta aikawa abokan hulɗarta, ta bayyana cewa daga ranar 28 ga Satumba za ta daina sayar da man fetur a Naira.
A cewar matatar, wannan mataki ya zama dole saboda sun riga sun sayar da fetur fiye da wanda suka saya da Naira, don haka ya gagara ci gaba da sayarwa a Naira.
Sai dai yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwarsu kan yadda rikici ke karuwa tsakanin matatar Dangote, dillalai da kuma wasu jami'an gwamnati.
Wani matashi mai kasuwancin fetur da aka fi sani da yan bunburutu, Kabir Abdullahi ya ce babu wani takamaiman farashin fetur a yanzu, musamman mu a nan Arewa.
Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa, Kabir ya ce hakan ya sa suke fama da mutane saboda karin da suke yi idan gidajen mai sun yi daga farashi.
"Ya kamata mahukunta au shiga tsakanin dillalai da matatar Dangoteda dukaau hannu a wannan rikicin, ya kamata kowa ya ajiye son ransa, a sa kasa a gaba.
"Talakawa na shan wahala gaakiya, duk abin da ke faruwa jan yan Najeriya yake karewa, ya kamata a kawo karshen duka rikici da matsalolin da auka shiga tsakanin masu ruwa da tsaki," in ji shi.
Matatar Dangote ta samu goyon baya
A wani labarin, kun ji cewa ɗan kasuwa kuma shugaban kamfanin Geregu Power Plc, Femi Otedola, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Matatar Dangote.
Wannan ya biyo bayan rikicin da ke tsakanin Matatar Dangote da kungiyar DAPPMAN, masu rumbunan ajiya da dillalan man fetur.
Otedola ya kuma yaba da matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya kawo sabuwar damar samun sauki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


